Taron ‘Kasashe biyu’ A Gefen Taron MDD A NewYork
Published: 27th, July 2025 GMT
A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin Taro a birnin New na kasar Amurka a dai-dai lokacinda ake gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Bin Farhan yana fadar haka.
Ministan ya kara da cewa a wannan taro nana saran shugaban kasar Faransa Emmanuel Mocron zai shelanta amincewar kasar faransa da kasar Falasdinu mai zaman kanta a kan iyakoki na shekara 1967. Wato yankunan da MDD ta amince a matsayin iyakokin HKI da kuma na Falasdinawa.
Yankunan dai sun hada da Gaza da yankin yamma da kogin Jordan,
Sai dai a halin yanzu gwamnatin HKI ta samar da dokoki wadanda suka tabbatar da kwace dukkan wadannan yankunan daga hannun Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Cilla Tauraron Dan’adam Mai Suna Nahid-2 A Yau
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya. Banda tauraron dan’adam na kasar Iran ita ma kasar Rasha tana da taurarin dana dam guda biyu a cikin kumbon wato Ionosfera-M3 da M4, sannan da wasu 18 na wasu kasashe.
Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika taurarin dan’adam na kasar Iran guda 3 wato Khayyam, Parsa -1 da kuma hudhod.
Manufar cilla Nahid -2 dai shi ne kyautata harkokin sadarwa na JMI a sararin samaniya. Kuma kamfanonin gina taurarin yan adama a cikin kasa ne suka hada kai don ganin ya kammala.