Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
Published: 1st, April 2025 GMT
Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi.
Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.
“A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.
Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.
“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.
A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Zan iya shiga mummunan yanayi idan Dangote bai aure ni ba’
Wata ’yar siyasa a jihar Bauchi mai suna Aishatu Haruna, ta ce ta shafe shekaru shida tana dakon soyayyar attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote a ranta, inda ta ce za ta iya shiga mummunan hali idan bai aure ta ba.
Ta ce sau uku tana yin mafarkin ta aure shi, kuma ba ta jin za ta iya auren wani ba shi ba a duniya.
A cikin wata tattaunawarta da gidan rediyon Albarka da ke jihar Bauchi, Aishatu, wacce aka fi sani da Gimbiyar Mawakan Bauchi, ta kuma ce sau uku tana zuwa kamfanin attajijin na Obajana, ko za ta hadu da shi a can.
Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura Lafiyar Tinubu kalau – SoludoAishatu wacce a 2019 ta yi takarar neman zama Majalisar Jiha dai ta wallafa hotonta ne dauke da katin gayyatar daurin aurenta da attajirin a shafukan sada zumunta, inda ta ce tana ganin ta wannan hanyar ce sakonta zai isa gare shi.
A cewarta, “Ita soyayya a zuci take, kuma ni na gamsu shi nake so, saboda yadda yake amfani da dukiyar da Allah ya ba shi wajen hidimta wa al’umma ba iya Najeriya ba, har ma da Afirka.
“Kusan shekara shida ke nan da farawar abin. Akwai lokacin ma da na yi tattaki na tafi har kamfaninsa na siminta da ke Obajana a jihar Kogi da nufin na gan shi har sau uku, amma bai yiwu ba.
“Dalilin da ya sa na buga katin shi ne saboda na san nan ce hanya mafi sauri da zai san da ni, kuma na san babu abin da ya gagari Allah,” in ji ta.
Sai dai ta tsaya kai da fata cewa ba don dukiyarsa take son shi ba, kawai ji ta yi shi kadai ne ya kwanta mata a ransa.
“Babu wanda aka haifa da dukiya, kuma ba don ita nake son shi ba, don haka ba maganar kwarya ta bi karya don baa bin da ya gagari Allah. Ni kawai yana burge ni ne,” in ji ta.
Ta ce ta gaji da dakon soyayyar a zuciyarta, shi ya sa yanzu ta fito da ita a shafukan sada zumuntar domin kada ta shiga wani halin.