Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja
Published: 27th, July 2025 GMT
Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja.
Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.
Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a DarazoKafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere.
Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsaGwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da Najeriya baki ɗaya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, ya ce Farfesa Gani ya taka rawar gani wajen bunƙasa Jami’ar Kashere.
“Farfesa Gani malami ne na ƙwarai, jagora kuma abin koyi wanda ya taimaka wa ɗalibai da jami’a. Mutuwarsa babban giɓi ne.”
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya sa aljanna ce makomarsa, tare da bai wa iyalansa da abokan aikinsa haƙuri da juriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Gani rasuwa Farfesa Gani
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.
“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”
Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.
“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.
Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.