Aminiya:
2025-07-27@18:16:14 GMT

Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP

Published: 27th, July 2025 GMT

Muƙaddashiyar Shugabar Jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce gwamnatin APC ce ta fi jefa ’yan Najeriya cikin talauci sama da kowace gwamnati a tarihin ƙasar nan.

Da ta ke zantawa da manema labarai a Jihar Kaduna, Sanatan ta ce jam’iyyar LP ta shirya tsaf don gyara kurakuran da gwamnatin APC ta tafka.

Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa

Ta roƙi ’yan Najeriya da su bai wa LP goyon baya, inda ta ce jam’iyyar za ta kawo canji na gaskiya.

Ta ce halin da ake ciki na wahala a ƙasar nan ya yi muni ƙwarai, kuma ta d6ora alhakin hakan kan gwamnatin APC.

Game da sauya sheƙa da wasu ’yan siyasa ke yi daga jam’iyyun adawa zuwa APC, ciki har da wasu daga LP, Sanatan ta bayyana hakan a matsayin abin takaici da rashin sanin darajar kai.

A cewarta, ba daidai ba ne mutum ya samu madafun iko da tallafin wata jam’iyya, amma daga baya ya koma wata jam’iyya don kawai samun riba ba.

Sai dai ta ce wannan ba zai girgiza jam’iyyarsu ba, domin ƙarfin jam’iyyar na ƙara bayyana da goyon bayan talakawan Najeriya.

Sanata Esther ta amince cewa jam’iyyar ta yi wasu kurakurai a baya, musamman wajen zaɓen ’yan takara da ba su dace da manufofin jam’iyyar ba.

Amma ta tabbatar da cewa sun ɗauki darasi, kuma suna shirin yin gyara kafin babban zaɓe na gaba.

“Yawancin waɗanda suka bar jam’iyyar ba su da cikakken ƙudirin kafa sabuwar Najeriya. Ficewarsu ta sa mun fi fahimtar juna kuma ta ƙara mana ƙarfi,” in ji ta.

Ta roƙi mambobin jam’iyyar da aka ɓata ws raj da su manta da saɓanin, su haɗa kai domin ƙarfafa jam’iyyar.

Ta ce ana shirin gudanar da zaɓen shugabanni a matakin ƙasa da kuma babban taron ƙasa kuma Majalisar Zartarwar Jam’iyyar (NEC) ta amince da waɗannan sauye-sauye da suke buƙata.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Najeriya Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Karyata Rade-radin Sayarda Makarantar Yusuf Dan-tsoho 

 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ana shirin sayar da makarantar firamare ta Yusuf Dantsoho da ke Unguwar Rimi GRA.

 

Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Maman Lagos, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar aiki makarantar.

 

Makarantar Yusuf Dantsoho, wacce aka kafa a shekarar 1920, tana tsakiyar Unguwar Rimi GRA, kuma ta samar da fitattun ‘yan Najeriya da dama da suka yi aiki a matakai daban-daban na gwamnati da kuma masu zaman kansu.

 

Alhaji Maman Lagos ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar sayar da wata cibiyar gwamnati, kama daga makarantu zuwa asibitoci.

 

Yace maimakon haka, gwamnati na da kudurin inganta da fadada irin wadannan cibiyoyin domin su fi amfani wa al’umma.

 

Alhaji Maman Lagos ya kalubalanci duk wanda ke da ikirarin ya sayi makarantar da ya fito da takardun shaida.

 

Ya ce gwamnatin Malam Uba Sani ba za ta sayar da makarantu mallakin gwamnati ba.

 

Haka kuma, ya bukaci iyaye da mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su kuma yi watsi da jita-jita marasa tushe.

 

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Muhammad Gambo, ya tabbatar da cewa makarantar Yusuf Dantsoho tana karkashin kulawar hukumar kananan hukumomi kamar yadda aka saba.

 

Wani jigo a harkokin makarantar, Abubakar Kantoma, ya bayyana cewa wasu ‘yan gine-gine sun yi yunkurin fara aiki a cikin harabar makarantar, amma aka dakatar da su saboda rashin bayyananniyar hujja.

 

Radio Nigeria ta kuma tattauna da wasu daliban makarantar wadanda suka nuna damuwa kan jita-jitar da ake yadawa.

 

Makarantar dai ta rufe ne a lokacin ziyarar saboda hutun karshen zangon karatu.

COV: Adamu Yusuf

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman
  • DR Congo: M23 Ta Yi Barazanar Kauracewa Sulhu da Gwamnatin Kongo
  • Gwamnatin Tarayya Ba Ta Soke Jarabawar WAEC Da NECO Ba
  • Asusun NADF, OCP Da Gwamnatin Katsina Sun Kaddamar Da Noman Hekta 50
  • Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki
  • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Karyata Rade-radin Sayarda Makarantar Yusuf Dan-tsoho 
  • Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu