Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-09-17@23:08:30 GMT

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Na Bana

Published: 27th, July 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Na Bana

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2025 tare da sabunta kudirin farfado da fiye da hekta 5,000 da ta lalace a fadin jihar.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a shatale-tale na Pentagon da ke Dutse babban birnin jihar.

 

Ya bayyana aikin dashen itatuwan a matsayin ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka domin ci gaban al’umma, inda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya muhalli da kare shi.

Ya ce: “Wannan yana da alaƙa da manufofinmu da suka shafi ƙaddamar da tsare-tsare da suka dace da kare muhalli, da ƙarfafa juriya da dorewar muhalli, da kuma inganta rayuwa mai tsafta da dorewa ga al’umma.”

Yayin da yake bayyana muhimmancin shirin, Malam Umar Namadi ya jaddada cewa kalubalen muhalli kamar ambaliya, sahara, sare itatuwa da kuma rashin daidaiton kula da shara na cigaba da barazana ga rayuwar mutane a jihar.

“Wannan barazana na shafar rayuwarmu ta yau da kullum, abincinmu, lafiyarmu, da kuma zaman lafiyar al’ummomi da dama a fadin jihar. Ya zama wajibi mu hada kai domin yaki da duk wani nau’in lalacewar muhalli.” In ji Gwamnan.

Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ya wakilta, ya bayyana cewa ana amfani da shirin ACReSAL wajen farfado da ƙasa ta hanyar dasa itatuwa, da kiyayewa da kuma tsarin noma da gandun daji.

“Yanzu haka, gwamnatin jihar Jigawa ta hanyar shirin ACReSAL na kokarin farfado da hekta 5,000 a wurare 27 a fadin jihar, ta hanyar samar da katanga ta itatuwa, wuraren kiwo da tsarin gandun daji. Mun riga mun fara sauya yanayin da ake ciki ta hanyar wadannan matakan da za a iya auna su.”

Ya kuma bayyana cewa an duba dokoki guda biyar da suka shafi muhalli kuma an miƙa su zuwa majalisar dokoki domin  gyara.

A cewarsa, dokokin da aka duba sun hada da Dokar Gandun Daji, Dokar Hana Kona Daji, Dokar Kiwon Dabbobi da Dokokin Tsafta.

Gwamna Namadi ya kara da cewa domin rage hadarin ambaliya da sarrafa ruwa, gwamnatin jihar ta sayi injina biyu masu iya aiki a ruwa da ƙasa domin kwance hanyoyin koguna da ciyawar Typha ta toshe.

“Baya ga wannan, gwamnati na aikin gina magudanan ruwa a wurare 32 daban-daban domin farfado da yankunan da ambaliya ta shafa. An kuma gina kilomita 130 na katanga a bakin rafuka domin rage ambaliya, kare gonaki da ƙarfafa ƙarfin gwiwar al’ummomin da ke cikin haɗari.”

Gwamnan ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga masu sare itatuwa da masu yin gawayi da su daina, ko kuma su fuskanci fushin doka.

“Ina amfani da wannan dama in gargadi duk masu sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, da masu yin gawayi da su daina. Kamar yadda muka ambata, mun duba dokokinmu na muhalli kuma mun tanadi hukunci mai tsauri ga duk wanda ya karya wadannan dokoki.”

Rediyon Najeriya ya bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ne ya jagoranci dashen itatuwan da kuma raba irin shukar ga ƙananan hukumomi.

Wannan wani bangare ne na tsare-tsaren kare muhalli na jihar, wanda ya haɗa da samar da irin itatuwa mmiliyan biyu da rabi a duk shekara, wayar da kai, da kuma haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da na ƙetare.

 

Usman Muhammad Zaria

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Itatuwa Jigawa Gwamnatin Jihar

এছাড়াও পড়ুন:

Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare

Fitattun dalibai akalla 12 ne  daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare  a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).

A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.

Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.

A cewarsa, an zabo daliban 12 ne  sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.

“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.

Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.

A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.

Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar