Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin duniya ba sabon labari ba ne, don haka mene ne abun mamaki idan ta bar UNESCO a karo na uku? Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana rayoyinsu ba su yi mamakin wannan matakin ba, lamarin da ke nuni da cewa, kasashen duniya sun saba da halayyar “kauracewar” Amurka.

Wannan mataki na “Amurka ta zamanto farko” yana kara ingiza bukatar tsarin damawa da mabambantan bangarori na hakika cikin hanzari.

Hujjar gwamnatin Amurka a wannan karon ta kasance a sarari, watau ta zargi UNESCO da ci gaba da zurfafa tabbatar da “mabambantan tsarin zamantakewa da al’adu” wadanda suka ci karo da manufarta ta “Amurka ta zamanto farko”. A cewar sakamakon binciken, kashi 93.5 na masu bayyana raayoyi sun soki Amurka bisa mayar da cibiyoyin kasa da kasa a matsayin kayan aikin cimma muradunta na siyasa.

Binciken jin ra’ayoyin ya nuna cewa kashi 90.7 cikin dari na wadanda suka bayyana raayoyinsu suna kallon ficewar baya-bayan nan a matsayin karin tabbaci na yadda Amurka ke nuna son zuciya saboda Isra’ila, yayin da kashi 91.1 cikin dari na jamaar da suka bayyana raayoyin nasu suka nuna cewa, tsarin mu’amalarta da hukumomin kasa da kasa bai zamo mai alfanu ga wata babbar kasa ba, ko kuma biyan bukatun kasashen duniya.

Wanda aka gudanar a kafofin CGTN na harsunan Ingilishi, da Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci, binciken ya tattaro raayoyin jamaa 9,097 cikin sa’o’i 24. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa

Wani babban Jami’in diblomasiyyar kasar Iran ya zargi Amurka da kuam HKI da laifin Zagon kasa ga dokokin kasa da kasa da kuma sabawa yarjeniyoyi da dokokin MDD.

Kazen Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia na kasa da kasa yana fadar haka a jiya Laraba a majalisar dinkin duniya a birnin NewYork na kasar Amurka, a lokacinda yake jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar Falasdinu.  

Gharibabadi ya bayyana cewa, Amurka da HKI sune manya-manyan masu haddasa rashin tsaro a kasashen yankin Asiya ta yamma.

Jami’in diblomasiyyar ya bayyana cewa Amurka da HKI ne suke haddasa halin da ake ciki a Gaza, na yuwan da kuma kisan kiyashi a Gaza da kashesu hanyar daukar yunwa a matsayin makami. Hakama tashe-tashen hankula a kasashen Yemen, Siriya da kuam Lebanon.

Banda haka wadanan kasashen biyu ne suka haddasa yakin kwanaki 12 a kan kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata.

Yace wadan nan kasashe ne suke haddasa matsaloli da ruda gidajen falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan, Yace HKI ta kori miliyoyin Falasdinawa daga gidajensu ta maidasu yan gudun hijira a kasashe makobta da kuma da sauran kasashen duniya,

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD
  • Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukan Matakin Kawo Karshen Dakatar Da Laifukan Kisan Kare Dangi A Gaza
  • Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
  • Matsalar Tsaro: Sarakuna Sun Bukaci Gwamnati Ta Canza Salo
  • Binciken CGTN: Masu Bayyana Raayoyi Na Turai Sun Gamsu Da Moriyar Cinikayya Tsakanin Sin Da Turai Sama Da Ta Turai Da Amurka
  • Kungiyar “Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Kasar Nijar Muammad Bazoum
  • Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi
  • Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
  • Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa