HausaTv:
2025-11-03@00:54:21 GMT

Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar

Published: 26th, July 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa JMI zata gaggauta ci gaba a fasahar tsaron kasa da kuma fasahar zamani a dukkan fagage bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a cikar kwanaki 40 da shahadar manya-manyan kwamandojin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliya a kasar.

Jagoran ya kara da cewa dukkan ilmomi tsaron kasa da kuma fasaha za su cilla da saura don samun ci  gaba.  A sakon da jagoran ya aikawa mutanen kasar ya yi tir da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar Iran, sannan yay aba da sojojin kasar Iran kan duka mai karfin da suka yiwa makiya.

Yace: Babu shakka an yi rashin manya-manyan kwamandojin sojojin kasar Kamar Bakiri salami, Rashid Hajizadeh shadmani da sauransu, abun yayi mana nauyi, hakama mun rasa masana fasahar Nukliya Tehranchi da Abbasi, amma kuma muna godiyar All..makiya basu cimma mummunan manufofinsu a kan Iran ba.  Yace: Manufar HKI na maida kasar Iran baya ya kasa kaiwa ga nasara,.  A ranar Jumma’a 13 ga watan yunin da ya gabata ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare a wurare da dama a cikin nan birnin Tehran. Inda suka kai wadannan manya-manyan mutane ga shahada. Sannan kafin kasar Yakin wanda suka nemi a tsaida shi sun dauki darasi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar

Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.

Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.

Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.

Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?