Matashi ya tono gawar kakarsa don yin tsafin kuɗi da ƙoƙon kanta
Published: 26th, July 2025 GMT
An kama wani matashi da ake zargi da tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa tare da sare kanta da nufin yin tsafin kuɗi a Jihar Naje.
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama mutumin mai shekaru 31 ne bayan dubansa ta cika a yankin.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya cewa wanda ake zargin tare da abokansa da suka taimaka masa ya tabbatar musu cewa zai yi tsafin kudi ne da ƙwarangwal din tsohuwar.
A cewar kakakin rundunar wanda ake zargin ya furta cewa yana neman tsafin ne don biyan bashin da ya kai sama da Naira miliyan biyu.
Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a FilatoA ranar 19 ga Yuli, 2025 ne jami’an ’yan sanda suka kama wannan gungun mutane da kai a otel ɗin Bida.
Babban wanda ake zargin ya tabbatar cewa kan kakarsa ce mai shekaru sama da 90 a lokacin da ta rasu kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Ya ce da farko ya samo kan ne bisa umarnin wani boka, don neman kuɗi cikin hanzari. Amma, bayan jin sharuddan tsafin, ya kasa bi, sai ya ɓoye kan na tsawon shekaru biyu.
Daga baya, abokinsa da wani kuma sun yi masa tayin sayenkan a kan Naira 100,000, kuma suka biya Naira 40,000 a matsayin kuɗin kafin alƙalami.
Daga nan suka kai wani wanda ake zargi da ninka kuɗi, da ya nemi Naira 500,000 don yin tsafin kuma sun biya shi da kaɗan-kaɗan.
Bayan an gama aikin, ya umarce su kada su buɗe ganga har sai ya gaya musu.
Makonni sun shude babu labari ko kuɗi sai suka yi masa takakkiya zuwa gidansa, amma ya shawo kansu cewa su haɗu a wani otel a Bida inda za su karɓi kuɗinsu.
A otel din ne kuma ’yan sanda suka kama su gaba ɗayansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Gawa ƙasarsa Tsohuwa zargi
এছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Bikin BIRTV2025 A Beijing
Yau Laraba, aka kaddamar da bikin nune-nunen harkokin rediyo da fina-finai da talabijin na kasa da kasa na Beijing karo na 32 ko kuma BIRTV2025 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda kamfanin CBIC na kasar Sin ya dauki nauyin shiryawa, bisa jagorancin babbar hukumar kula da harkokin rediyo da talabijin ta kasa gami da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasa wato CMG.
Bikin na BIRTV2025 yana kokarin kafa wata gada don inganta mu’amala tsakanin kasa da kasa ta hanyar gudanar da harkokin kasa da kasa, ciki har da taron sanin makamar aiki don inganta kwarewar kafafen yada labaran Sin da Afirka, wanda zai mayar da hankali kan irin labaran da suka kamata a watsa, gami da hanyoyin watsa su, tare kuma da lalubo sabbin hanyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin masana’antun talabijin da rediyo.
Bikin BIRTV2025 na bana wanda za’a rufe shi a ranar 26 ga wata, ya samu halartar kamfanoni sama da 500 daga kasashe da yankuna fiye da 20, wadanda suke nuna sabbin nasarori da fasahohin da suke da su a sana’o’in da suka shafi rediyo da fina-finai da talabijin da kuma intanet. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp