Jihar Jigawa Na Kara Bullo Da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Bukata Ta Musamman
Published: 25th, July 2025 GMT
A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu.
A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya.
Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin.
Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za ta bada hadin kai domin samun nasarar shirin a yankin.
A cewar sa, an samu karin alawus na masu bukata ta musamman daga naira dubu 7 zuwa dubu 10.
Shi ma a nasa, jawabin, jami’in shirin na yankin, Mallam Mansir Dahiru yace suna tantance masu bukata ta musamma da suka cancanta domin amfana da shirin a Karamar Hukumar ta Birnin Kudu.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Karamar Hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Masu Neman Takarar Shugaban Kasa A PDP Sun Kara Matsa Kaimi Bayan Ficewar Atiku
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar.
Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar.
A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027.
A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa na wucin gadi da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa na wucin gadi.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa Makinde da Bala Mohammed su ne manyan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a yanzu haka, yayin da ake sa ran wasu jiga-jigan jam’iyyar za su biyo baya kafin zaben 2027.
Majiyar ta ce, “Ana tambayar game da wadanda suka nuna sha’awarsu na neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyya a halin yanzu. Duk da dai ba su fito fili sun bayyana ba, mun ji daga wurin shugabannin jam’iyyar, cewa Makinde da Bala Mohammed har ma da wasu tsoffin gwamnonin daga Kudu suna da sha’awar neman tikitin shugaban kasa jam’iyyar PDP a 2027.
“Amma a hakikanin gaskiya, a yanzu haka ba za mu iya sanin adadin wadanda suke sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a PDP, sai idan lokaci ya yi duk za a san su. Don haka, jam’iyyar PDP ta bude kofarta ga kowa, kuma ta kasance jam’iyyar da ke da karbuwa sosai a tsakanin ‘yan Nijeriya.”
Wani jigo a jam’iyyar wanda ya nemi a Sakaye sunansa don ba a shi izinin yin magana a hukumance ba, ya goyi bayan bude tikitin takarar shugaban kasa a PDP a 2027 ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Shi kuwa, tsohon mataimakin shugaban PDP na yankin kudu maso yammaci, Eddy Olafeso, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyyar sun dauki darashi ga abubuwan da suka faru a baya.
Yayin da tsohon sakataren jam’iyyar na kasa, Ibrahim Tsauri, ya shawarci mambobin jam’iyyar cewa su bar uwar jam’iyyar ta yanke hukunci, sannan kuma ya yi gargadi kan kauce wa bin tsarin karba-karba.
A nasa martanin, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim ya ce Shugaban Tinubu zai kayar da Makinde, Bala Mohammed, ko wani dan takarar da PDP ta tsaida a 2027.
Ibrahim ya bayyana cewa, “Makinde da Bala Mohammed ba su da wata gogewa a matakin kasa na siyasar Nijeriya. Wadannan gwamnonin biyu ba za su iya jure fafatawar siyasar kasa nan ba. Ba su da gogewar da dan takararmu yake da shi.
“Mutane da ka ambata ba su da ikon doke shugaban kasa a kowanne fanni na siyasa. Wannan ba matsala ce da za ta ba mu ciwon kai ba. Koma dai wane yanki PDP zai fitar da dan takarar shugaban kasa ba zai yi nasara ba a 2027.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp