Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje
Published: 26th, July 2025 GMT
Yau Juma’a, 25 ga Yulin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi takardun nadi daga sabbin jakadun kasashe 16 da suka hada da Angola, da Benin, da Sudan ta Kudu, da Amurka, da Iran, da Chile da sauransu a Babban Zauren taruwar Jama’a dake nan birnin Beijing.
Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin tana darajanta dangantakar abota da al’ummomin duniya, kuma tana fatan kara hadin gwiwa a mabambantan bangarori, da kowace kasa bisa mutunta juna, da daidaito da samun moriyar juna.
Xi ya kuma jaddada cewa, a bana ake cika shekaru 80 tun bayan da Sin ta samu nasarar yakin kin harin Japan, da kuma yakin duniya na biyu, kana ake cika shekaru 80 da kafuwar MDD. Don haka Sin ke fatan kara hada hannu da kasashen duniya, ta yadda za su kare tsarin duniya, da dokar duniya bisa tushen majalisar, don ta zama mai kiyaye hadin gwiwa, kuma mai ingiza cudanyar al’adu, mai kafa kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন: