Aminiya:
2025-11-03@04:03:12 GMT

Super Falcons sun lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko

Published: 27th, July 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, ta sake kafa tarihi bayan ta doke ƙasar Maroko da ci 3–2 a wasan ƙarshe na gasar WAFCON.

Yanzu haka Super Falcons ta lashe kofin karo na 10, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta taɓa lashewa a tarihin gasar.

ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba

Maroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu cikin mintuna 25 ta hannun Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayan Super Falcons a filin wasa na Rabat.

Amma Najeriya ba ta karaya ba.

A minti na 64, Esther Okoronkwo ta warware ƙwallo a bugun fenariti, sannan ta taimaka wajen cin ƙwallo ta biyu da Folashade Ijamilusi ta jefa a minti na 71.

Saura minti biyu a tashin daga wasan, Jennifer Echegini ta ci ƙwallo ta uku, wanda hakan ya sa ta girgiza duniyar ƙwallo.

Wannan nasara ta tabbatar da mamayar da Super Falcons ta yi a Afirka.

Ƙungiyar ta lashe dukkanin wasanim ƙarshe da ta buga a gasar WAFCON, kuma yanzu tana da kofuna 10 a tarihin gasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ƙwallo Maroko Najeriya WAFCON

এছাড়াও পড়ুন:

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025?
  • Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
  • Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA