Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD
Published: 25th, July 2025 GMT
Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya yi magana a wani taro na bude kofar Kwamitin Sulhu na MDD game da hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwar kasashen Musulmi (OIC), inda ya karyata batun da wakiliyar Amurka ta yi game da yankin Xinjiang na Sin.
Fu Cong ya ce, Sin ta nuna adawa kwarai tare da kin amincewa da zargi mara tushe balle makama da wakiliyar Amurka ta yi game da Xinjiang.
Fu Cong ya kuma bayyana cewa, a cikin shekaru shida da suka gabata, sama da kasashe 100, ciki har da kasashe masu bin addinin Musulunci da dama, sun nuna goyon bayansu ga madafun iko na Sin a kwamiti na uku na babban taron MDD da nuna adawa da siyasantar da batun kare hakkin dan Adam da kuma amfani da shi a matsayin hanyar tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe. Wannan ya tona asirin makircin Amurka na “amfani da Xinjiang don hana ci gaban Sin”, kuma mugun nufinta na tayar da husuma a tsakanin kasashe ya ci tura. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo.
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a RibasMajiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato makamai da dama daga hannunsa, ciki har da bindigogi kirar Turai, harsasai, kakin sojoji da na ’yan sanda.
“Cafke wannan kwamanda babban ci gaba ne wajen murƙushe ayyukan ta’addanci da ƙungiyar IPOB ke aikatawa, musamman a yankunan da suke hana zaman lafiya,” in ji majiyar.
Kungiyar IPOB, wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya don kafa ƙasar Biyafara, ta kasance a gaba-gaba wajen aikata hare-hare da ta da tarzoma a jihohin kudu maso gabas, musamman ta hannun sashen rundunar da suka kafa da kansu mai suna Eastern Security Network (ESN).
Ana dai zargin cewa Eze yana ɗaya daga cikin jagororin da ke tsara harin kwantan bauna, da hana zirga-zirga a wasu sassan yankin, wanda hakan ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman ɗar-ɗar.
Wannan nasara na zuwa ne bayan makonni kaɗan da wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa Simon Ekpa, wani babban jigo a ƙungiyar IPOB, hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan yari kan laifukan da suka shafi ta’addanci da tayar da zaune tsaye.
Masu sharhi na ganin cewa cafke Gentle de Yahoo wata alama ce da ke nuna cewa ana shirin ragargaza ƙungiyar IPOB gaba ɗaya, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman ganin cewa wasu sassan yankin na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.