Kasar Iran Ta Ce Tana Hulda Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani
Published: 27th, July 2025 GMT
Kasar Iran ta bayyana sake kulluwar hulda da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya sanar da cewa: Wasu kasashe na tuntubar Iran da Amurka a matsayin masu shiga tsakani.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa ya shaidawa tashar Haber Turk ta Turkiyya cewa: Akwai tuntuba tsakanin Iran da Amurka ta wasu kasashe masu shiga tsakani, yana mai cewa: “Wasu kasashe suna hulda da Iran da Amurka, kamar yadda kuka sani, don haka Iran tana tattaunawa da Oman a matsayin mai shiga tsakani.
Da yake amsa tambaya game da ganawar da kungiyar Tarayyar Turai a Istanbul, ya ce: “Iran ta sake gudanar da wani zagaye na shawarwari tare da kasashen Turai a matakin mataimakan ministoci. An dade ana ci gaba da gudanar da wannan tsari, tana ganawa da tattaunawa kan batutuwa daban-daban kan batun makamashin nukiliya. A taron jiya sun tattauna batutuwan fasaha na batun makamashin nukiliya da kuma batun dage takunkumin da aka sanyawa kasar Iran, kamar yadda Iran din ta jaddada cewa dole ne a samar da duk wani bangare na inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ayatullahi Makarem Shirazi Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Hadin kai Da Suka Bayar Lokacin Yakin Kwanaki 12
Ayatullah Makarem Shirazi ya jaddada cewa: An kara samun karfafan hadin kan al’umma Iran bayan wuce gona da irin ‘yan sahayoniyya da Amurka kan kasarsu
Ayatullah Nasser Makarem Shirazi, babban malamin addinin Musulunci a birnin Qum mai tsarki na kasar Iran ya jaddada cewa: An kara samun hadin kan kasa bayan yakin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A yayin ganawarsa da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a jiya Laraba a birnin Qom mai alfarma Ayatullah Makarem Shirazi ya yi ishara da yakin tunani da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya da Amurka suka yi kan Iran yana mai cewa: Wadannan makiya sun yi zaton za su haifar da rudani ta hanyar kai wa Iran hari, amma alhamdulillahi ba wai kawai hakan ya faru ba, amma hadin kan al’ummar kasar ya kara karfafa. A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Makarem Shirazi ya bayyana wasu manyan matsaloli guda uku da al’umma ke fuskanta: hauhawar farashin kayayyaki, gidajen haya, da samar da ayyukan yi ga matasa. Ya ce, “Dole ne a yi kokarin magance wadannan matsalolin, kuma in Allah idan ya yarda za a yi nasara.”