Manoma A Kirikasamma Sun Yaba Wa Gwamna Namadi Bisa Rangwaman Takin Zamani
Published: 27th, July 2025 GMT
Duba da tsadar kayayyakin noma da ke kara ta’azzara a fadin kasar nan, da kuma janye hannun manoma da dama daga noman shinkafa da masara sakamakon tsadar taki,Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kaddamar da rangwamin kashi 45 zuwa 50 cikin 100 na farashin buhun taki, tare da tura manyan motocin daukar kaya domin rarraba takin a kananan hukumomi 27 na jihar.
Rediyon Nigeria ya ruwaito cewa, karamar hukumar Kirikasamma ta karbi buhuna 1,200 da za a sayar wa manoma a farashi mai rangwame.
Shugaban sashen aikin gona da albarkatun kasa na karamar hukumar, Alhaji Sabi’u Kani, ya bayyana cewa za a sayar da buhun takin NPK na kamfanin Solar Brand a kan 28,800.
Yayin kaddamar da fara sayar da takin a gundumomi 10 na Kirikasamma, Shugaban karamar hukumar, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya ce wannan mataki na Gwamna Namadi na nufin rage wa manoma radadin tsadar taki a kasuwanni.
Marma ya kara da cewa, “Kwamitocin gundumomi karkashin jagorancin kansiloli za su jagoranci rabon takin, tare da sauran mambobi na kowace gunduma.”
Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Manoman Najeriya (AFAN) reshen Kirikasamma, Kabila Suga, ya jinjinawa shugaban karamar hukumar da Gwamna Umar Namadi bisa wannan rangwame da zai taimaka wa manoma.
Kabila ya kara da cewa farashin buhu daya ta NPK a kasuwa ya kai kimanin Naira 50,000 zuwa 56,000, wanda ya fi karfin yawancin kananan manoma.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa karamar hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a.
Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu.
Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga mutane da birane.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da wata ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta Janar na birnin Dubai inda suka tattauna batutuwan haɗin gwiwa a fannin kirkirar makamashin sharar gida da kula da sharar gida ta zamani, da kuma tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
A ganawar, duk Bangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin jihar Kaduna zuwa tattalin arzikin mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Jihar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun ƙasashen duniya wajen yin haɗin kai, ƙirƙira, da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa da ci gaban kowa da kowa a fadin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA