Burtaniya Zata Fara Jefawa Falasdinawa Abinci Daga Sama
Published: 26th, July 2025 GMT
Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa ya fara tuntubar wasu kasashen turai kan nshirin jefawa Falasdinawa abinci daga sama tare da taimakon kasar Jordan.
Shafin yanar gizo na Arab News ya nakalto Starmer yana fadar haka a yau Asanar ya kuma kara da cewa ya yi magana da kasashen Faransa da Jamus kan wannan shirin.
Labarin ya kara da cewa banda jefa masu abinci kasashen zasu sauka su dauki marasa lafiya musamman yara kanana don jinyarsu..
Tun kimani watanni 4 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rufe kofofin shiga zirin gaza ta kuma hana shigowar abinci da magunguna, da nufin kashe dukkan falasdinawa kimani miliyon biyu a Gza, don ginawa yahudawa matsugunai a yankin.
Tun fara yakinn tufanul aksa a ranar 07 ga watan Octoban shekara 2023 ya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da dubu 60 a yayinda wasu fiye da dubu 150 suka ji rauni.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta.
Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo“Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna cewa ba sa son a samu hamayya a lokacin zaɓe,” in ji shi.
Galadima ya kuma yi gargadi kan shirin nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin rudani.
“Ina fatan ba gaskiya ba ne, domin idan wannan mutumin ya zama shugaban INEC, ka tabbata cewa wannan gwamnati na neman tayar da yaƙin basasa,” in ji shi.
Sai dai bai ambaci sunan mutumin ba.
Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.
“Wannan batun fara yaƙin neman zaɓe kafin INEC ta ba da izini, gwamnatin da ke kan mulki ce ta fara shi. Wannan yana nuna cewa INEC ba za ta iya zama mai adalci a irin wannan yanayin siyasa da muke ciki ba,” in ji shi.