HausaTv:
2025-07-26@09:47:38 GMT

An Watse A Taron EU Da China Saboda Ricikin Kasuwanci Da Siyasa  Tsakaninsu

Published: 25th, July 2025 GMT

An takaita taro tsakanin kasashen turai da China a birnin Beijin zuwa ranar Alhamis kadai bayan da bangarorin biyu sun sami sabani a tsakaninsu kan al-amuran kasuwanci.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron har na tsawon kwanaki uku amma kwotsom sai kasar China ta bukaci a takaita taron zuwa jiya Alhamis kadai.

A nata bangaren shugaban tarayyar ta turai Ursula von der Leyen  ta bayyana cewa, kasat China ce kadai take amfani da tsarinn kasuwancin da ke tsakanin bangarorin biyu, ta bada misali da cewa bambancin ribar da china take samu a cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai Euro biliyon 305.8 ko dalar Amurka biliyon 360 a shekarar da ta gabata kadai. Sannan harkokin kasuwanci a tsakanin Eu da China yana karuwa kamar yadda bambanci da rashin daidaito yake karuwa. Don haka tace dole ne a sauya tsarin. Amma gwamnatin kasar China ta ce rashin daidaito a harkokin kasuwanci tsakanin bangarorin biyu ba daga kasar China ya taso ba, saboda kasashen Eu suna harkokinnwasuwanci da kasashen duniya da dama. Shugaban kasar China Xi Jinoing ya bukaci kungiyar EU ta gyara harkokin kasuwancinta da kanta.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar China

এছাড়াও পড়ুন:

Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China

Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China.

Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi ne ranar Alhamis ba tare da ko mutum daya ya rayu ba.

“Ma’aikatan ceto sun gano wasu sassan jirgin na ci da wuta,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito jami’an ceton na cewa.

Reuters ya kuma ce jirgin wanda mallakin kamfanin Angara Airlines ne, ya fadi ne a kusa da Tyndra, wani gari da ke yankin na Amur, bayan hanyar da yake magana da masu kula nda zirga-zirgar jirage a sararin samaniya ta katse.

Kazalika, kamfanin dillancin labaran Rasha na Interfax, ya ce jirgin ya fadi ne a yunkurinsa na sauka a karo na biyu bayan ya kasa sauka a karo na farko a filin jiragen saman a Tyndra.

Kamfanin ya kuma rawaito cewa rashin kyawun yanayin gani ne a lokacin sauka ne ya haddasa hatsarin.

Sai dai bayan faduwar jirgin yak ama da wuta, kuma ana zargin babu ko mutum daya da ya rayu, kamar yadda wani faifan bidiyo a wajen da jirgin ya fadi ya nuna

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kamfanin na Angara bai kai ga fitar da cikakken bayani kan musabbabin hatsarin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Ta Ci Gaba Da Inganta Sinadarin Uranium
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: Taro Tsakanin Iran Da Tawagar Kasashen Turai Dama Ce Ta Gyarar Tunanin Tarai
  • Iran da Bangladesh sun bukaci taron gaggawa na OIC kan kisan kiyashi a Gaza
  • Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
  • Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  •  Iraki Ta Yi Watsi Da Bukatar Amurka Akan Dakarun Sa Kai Na” Hashdus-sha’abi”
  • Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa