Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA
Published: 26th, July 2025 GMT
Wani abin karin farin ciki shi ne, yadda masu rauwa da tsaki a fannin, suka jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya zabo ya kuma nada Dantsoho, a matsayin shugaban NPA, inda akasarin su, suka yi ittifakin cewa, zabo, bai zama zabar Tumun dare ba, musamman duba da irin dimbin ci gaban da yake ci gaba da samar wa a fannin, a cikin shekara daya kacal.
Gyaran Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar:
Tun bayan da ya dare karagar shugabancin NPA Dantsho ya lashi Takon, inganta ayyukan Tashoshin, inda ka fara da tattara bayanan ayyukan da ya kamata ayi da kuma fara yin aikin gadan-gadan, inda aka ware dala bilyan daya, domin fara gyran Tashar Tincan Island, ta Apapa, ta Onne da ke jihar Ribas, ta Warri da kuma ta Kalaba.
Aikin Fadada Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar:
A karkashin shugabancin na Dantsoho na NPA, ya dauki sabbin kwararan matakai domin fadada ayyukan na NPA, inda a watan da ya gabata, Dantsoho, ya jagoranci tawagar sauran mahukuntan NPA, kan rattaba hannun yarjejeniyar, dala biliyan daya don bunkasa aikin Tashar Snake Island, don a samar da hekta guda 85, don gudanar da hada-hadar shiyya ta shige da ficen Jiragen Ruwa.
Kazalika, akwai kuma aikin Tashoshin Badagry na Ondo da kuma na Burutu, wadanda a yanzu, suka kai matakin kammala wa.
Samar Da Kyakyawan Tsarin Ajiye Kwantaina A Tashshin Jiragen Ruwa:
A karkashin shugabancin sa, NPA ta zama mamba a kungiyar IPCSA, wanda hakan, ya bai wa kasar damar wanzar da aikin NSW.
Dantsoho, ya tabatar da an samar da tsarin gudanar da ayyuka na bai daya, wato NSW wanda shi ne, ake gudanarwa, a daukacin fadin duniya, musamman wajen samun musayara bayanai, na zirga-zirgar kayan da Jirage suka yo dakon su, ko dai ta ruwa, ko ta sama ko kan tudu.
Yin Amfani Da Na’urori Don Magance Cunkoson Motoci A Tashoshin Jiragen Ruwa:
Kirkiro da yain amfani da na’urorin rage cunkoson motocin da ke shiga cikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasa, da a karkashin shugabancin Dantsoho, hakan ya taimaka matuka wajen rage cunkoso a daukacin Tashoshin kasar, musamman duba da yadda, aka samar da guraren da za a rinka ajiye motocin.
Kazalika, an yi hakan ne, domin a samar saukin gudanar da hada-hadar kasuwanci ta yau da kullum a Tashoshin.
Kara Bunkasar Fitar Da Kaya Ketare Da Habakar Kasuwanci:
Sakamakon kara inganta Tashoshin Jiragen Ruwan kasar a karkashin shugabancin Dantosho, hakan ya sanya hada-hadar kasuwancin kasar, a zango na uku na 2024, Nijeriya ta samu Naira tiriliyan 5.81 wadanda suka yi, daidai da dala bilyan 3.7.
Bugu da kari, bisa nasarar da aka samu ta wanzar da tsarin sayar da Danyen Mai da sauran Dangogin Mai kan farashin Naira, da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a yi, hakan ya sanya, Nijeriya ta samu damar adana biliyoyin kudaden musaya na kasar waje.
Kazalika, hakan ya sanya, an rage dogaro da shigo Man daga waje, wanda kuma hakan ya kara yawan albarkatun makamashi na kasar, tare da samar da ayyukan yi, na kai tsaye, da wadanda ba na kai tsaye ba.
Hakazalika, a Hukumar NPA a karashin shugabancin Dantsoho, ta sanya batun hadaka da kamfanoni masu zaman kansu wato kan tsarin PPP, wanda hakan ya kara yawan kudaden shigar da take Tarawa.
Shigar Nijeriya Cikin Kungiyar Kula Da Tashoshin Jiragen Ruwa Ta PMAWCA
A lokacin shugabancin sa ne, Nijeriya ta shiga cikin sahun sauran kasashen da ke Afirka ta Yamma na sufurin Jiragen Ruwa, inda aka zabi Dantsoho a matsayin Shugaban kungiyar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afirka Yamma wato PMAWCA.
Kazalika, ta hanyar zabar sa ne, ya sanya tun bayan kafa kungiyar a 1972 aka samu dan Nijeriya na farko, da zama Shugaban kungiyar.
NPA ta taimaka matuka, wajen samar da shawarari kan kara yawan sufurin Jiragen Ruwa daga Tashar Lekki, zuwa sauran kasashen, da ke makwabtaka, da Nijeriya.
Kara Samar Da Masu Zuba Hannun Jari:
Duba da irin kwarewar da ya samu, musamman a lokacin da ya rike mukamin Manaja na Tashar Onne, wanda a lokacin ya samar da huddar abotakar kasuwanci a Tashar ta Onne, a kwanna baya Dantsoho ya kai ziyarar aiki, a Tashoshin NPA da ke a Gabashin kasar, musamman idan ya nuna bukatar samar da masu son zuba hannun jari, a Tashohin Ribas, Kalaba da ta Burutu.
Hakan ya sanya, kamfanonin da ke yin dakon Kwantainoni, musamman na yankin Yammacin Afirka wato WACT-APM, suka kadammar da ayyukansu.
Kazalika, an gudanar da aikin ne, bisa hadaka da kamfanin Hapag-Lloyd.
Hakan ya kuma kara bunkasa hada-ahadar kasuwanci a kan lokaci, musamman ga Jiragen da ke sauka a gabashin kasar.
Rahoton Kididdigar Ayyuaka A NPA:
Bisa rahoton kididdiga na mahkuntan NPA a 2024, ya nuna cewa, an samu gagarumar ci gaba a bangarori da ban da ban a NPA, wadanda suka hada da; gudanar da ayyuakn zirga-zirgar kananan Jiragen Ruwa da sauransu.
A 2024, NPA ta kara samun yawan Jiragen dakon kaya da ke zuwa Tashoshin Jiragen ruwan kasar, inda suka karu daga kaso kaso 45.1 zuwa kaso 71,213,197, wanda kuma hakan ya nuna cewa, yawan hada-hadar kasuwancin da aka gudanar, sun kara ayyukan na NPA.
Jiragen da ke tsaya wa a Tashar Lekki, sun karu zuwa kaso 2,160.8, inda kuma wadanda ke tsayaw a Tashar Onne, suka karu zuwa kaso 9.4%, sai kuma na Tashar Tin Can Island, da suka karu zuwa kaso 7.3.
Samun Karin Jiragen Ruwa Da Ke Zuwa Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar:
Yawan Jiragen Ruwa da ke zuwa Tashoshin sun karu daga kaso 5.6 zuwa kaso 3,791 a 2023, inda kuma a 2024, suka karu zuwa kaso 4,005.
Hakan ya nuna yadda aka samu karin yawan masu yin rijista da suka kai, karin kaso 15.4, wanda hakn yah aura, daga tan na kaya 123,660,278 zuwa tan to142,660,418.
Tashar Lekki ta kasance kan gaba, inda aka yi rijistar Jiragen da ke zuwa Tashar suka karu zuwa kaso 477.6, sai ta Onne, ta samu karin kaso 5.8.
Jimlar Kwantainoni da ake sauke wa a Tashar sun karu zuwa kaso 9.7 a 2024, idan aka kwatatan da na 2023.
Kazalika, karin Kwantaononin da ke fitar da su, sun karu zuwa 53.7 daga kaso 12.2.
Bugu da kari, yawan sauran Kwantainonin da ke fitar da su, sun karu zuwa kaso 136.5.
Zirga-Zirgar Kananan Jiragen Ruwa Ta Karu:
Ayyukan zirga-zirgar kanannan Jiragen Ruwa a Tashoshin Jiragenn Ruwan kasar, ya karu zuwa kaso 49.6, inda kuma yawan Jiragen daga 8,956 da ake yin amfani da su a 2023, suka karu zuwa 13,396 a 2024.
Hakazalika, karin wadanda suka yi rijista na GRT, sun karu daga kaso 129.3 zuwa kaso 1,997,163 sai kuma wani karin kaso 4,579,742.
Dantsho ya tabatar da ya daidaita iya lokacin zuwan Jiragen Ruwa ga Tashoshin da kuma lokacin da ya kamata su juya, musamman domin a rage cunkoson Jiragen Ruwa a Tashohin wanda wanda hakan ya sanya aka samu gudanar da ayyuka a Tashoshin da suka kai kaso 1.0.
Musamman a Tashar Lekki wadda ta kasance a cikin kwanuka 2.5 kacal, ake samun Jiragen da ke zuwa suna kuma juyawa, bayan sun sauke kayan da suka yi dako.
Yawan lokutan zuwa da juyawar Jiragen a 2023, ya kai kaso 30.1, wanda a 2024, ya karu zuwa kaso 33.
Tabbara Da Walwala Da Jin Dadin Ma’aikata:
Dantsoho ya mayar da hankali wajen inganta jin dadi da walwalar ma’aikan NPA a matsayin daya daga cikin muradun shugabancinsa, musamman ta hanyar yin hadaka da kunyoyin ma’aikatan irinsu, MWUN da kuma SSASGOC.
Hakan ya sanya, kungiyoyin suka kuma yabawa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola da kuma Dantsoho saboda kawo karshen matsalolin da suka dakele su, na samun ci gaban da ya kamata su samu da sauransu, musamman samun jarrabawar karin girma, a NPA.
Samun Jinjina Da Yabo:
Hatta daga gun Dangote da sauran masu ruwa da tsaki da kuma sauran kamfanoni, Dantsoho ya samu yabon su da kuma jinjinar su saboda irin irin kokrin da yake yi na ciyar da NPA gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tashoshin Jiragen Ruwan kasar A Tashoshin Jiragen Ruwa a karkashin shugabancin A karkashin shugabancin suka karu zuwa kaso Jiragen Ruwa Da Jiragen Ruwa da hakan ya sanya Hakan ya sanya Jiragen da ke sun karu zuwa Tashar Lekki Dantsoho ya
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.