An Kashe Sojojin HKI 3 A Yankin Khan-Yunus Na Gaza
Published: 27th, July 2025 GMT
Da safiyar Yau Lahadi Adadin sojojin mamaya na HKI da aka kashe a yankin Khan-Yunus sun kai 3.
Jaridar Yediot Ahranot ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa; An kuma kashe waji jami’in soja na rundunar Gulani ta hanyar fashewar nakiya da aka dasa akan hanyar motarsa a jiya Asabar a Kudancin Gaza.
Har ila yau jaridar ta ce, an kuma jikkata wani jami’in sojan mamayar bayan da nakiya ta daki wata motar jigilar sojoji.
A nata gefen, rundunar Kassam ta kungiyar Hamas ta sanar da kai wa motar daukar sojojin HKI hari ta hanyar nakiyar da ta dasa a gidan gaban motar.
Bugu da kari dakarun na Kassam sun sanar da kai wani harin akan motar soja ta 3 ta hanyar amfani da makamin “al-Yassin 105” a yankin Abasan al-Kabirah dake Khan Yunus.
Haka nan kuma dakarun na Kassam sun ce, mayakansu sun ga yadda sojojin na mamaya su ka binne motocin da su ka kone, da kuma saukar jiragen sama masu saukar angulu domin daukar gawawwaki da wadanda jikkata.
Duk da cewa sojojin na HKI sun dauki shekaru biyu suna kisan kiyashi a Gaza, sai dai duk da haka bai hana ‘yan gwgawarmaya fitowa suna kashe su da jikkata su ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza
Kakakin rundunar tsaron Isra’ila ya ce suna aiki tare da la’akari da dokokin duniya, inda ya ce Hamas na boye “makamai” a cikin fararen hula, sannan suna “rusa gine-gine ne kawai idan ta zama dole.”
An gani a zahiri yadda Rafah ya lalace a kusa da bakin iyakar Masar
A ‘yan makonnin da suka wuce, sojojin Isra’ila da ‘yan kwangilar rusau sun sanya alamar rusau a gidaje da dama
Nazarin masa irin su Corey Scher da Jamon Ban Den Hoek ya nuna cewa barnar da aka yi a Gaza tun daga watan Afrilu ya yi muni a yankin.
Akwai manyan motocin katafila jigbe a yankunan
A watan Yuli, ministan tsaron Isra’ila, Katz ya bayyana tsare-tsarensu na kafa abin da ya kira “birnin aikin ceto” a Rafah, inda za a fara da ajiye Falasdinawa 600,000 a sansanin.
Yunkurin na shan suka sosai. Tsohon firaministan kasar, Ehud Olmert ya shaida wa BBC cewa tsarin zai yi kama “kafa sansanin ajiye wadanda ba a so.”
Tel al-Sultan na cikin biranen da suka fi yawan mutane a yankin Rafah. Akwai tarin mutane kuma a garin ne asibitin kula da yara da marayu da yaran da aka tsinta suke rayuwa.
Hotunan tauraron dan’adam da ke nuna yadda hare-haren sojojin Isra’ila ya barnata yankin duk da akwai gomman gine-gine da suka tsira.
Zuwa ranar 13 ga Yuli, hare-haren sun riga sun munana, inda ake samun manyan gine-gine sun rufta baki daya. Asibitin na cikin ‘yan tsirarun gine-ginen da suka rage.|| Haka kuma an sanya alamar rusau a gine-ginen da ke kusa da garin Saudi – garin da ke dauke da babban masallaci da makarantu da dama.
Wani faifan bidiyo da aka tabbatar ya nuna wata tanka na tafiya a titin Rafah wasu ma’aikata kuma suna diga.
Haka kuma Isra’ila ta yi rusau a wasu sassan zirin wadanda suka tsira daga hare-haren farko.
Birnin Khuza’a da ya yi fice da noma, wanda ke da da nisan kilomita 1.5 (mil 0.9) daga bakin iyakar Isra’ila.
Kafin fara yakin, birnin na da mutum 11,000, kuma yana da kasar noma mai kyau da ake noma tumatir da fulawa.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta rusa gine-gine 1,200 a Khuza’a, wadanda ta yi zargin kadarorin “‘yanta’adda” ne da Hamas ke amfani da su.
An samu labarai irin haka a birnin Abasan al-Kabira, inda kusan mutum 27,000 ke rayuwa kafin yakin. Hotunan da aka dauka a 31 ga Mayu da 8 ga watan Yulin sun nuna yadda aka daidaita yankin a cikin kwana 38.
Isra’ila ta kirkiri “sansanonin tsaro” a tsakanin wasu yankunan Gaza, kuma ta lalata gine-gine da dama a tsakanin su. Wurin da ta kai farmaki na kusa-kusan nan shi ne gab da gabashin Khan Younis, ciki har da Khuza’a da Abasan al-Kabira.
Haka kuma tun farkon yakin, masana suke hasashen Isra’ila na yunkurin kafa “cibiyoyin tudun mun tsira” ta hanyar rusa gine-gine da ke gab da bakin iyakarta.
A Kizan Abu Rashwan – yankin da ya yi fice da noma mai nisan kusan kilomita 7 daga bakin iyakar Isra’ila – kusan kowane gini da ke tsaye an rusa shi daga ranar 17 ga Mayu.
Sashen BBC Berify ya gabatar da sakamakon bincikensa ga IDF ciki har da wuraren da ta rusa, inda aka bukaci ta yi bayani, amma ba ta yi ba.
“Kamar yadda aka sani ne, Hamas da sauran kungiyoyin ‘yanta’adda na boye makamai a cikin fararen hula,” in ji kakakin IDF. Sannan ya kara da cewa IDF na “ganowa tare da barnata kadarorin ‘yanta’adda da suke cikin gine-ginen ne.”
Lauyoyin kare hakkin dan’adam da dama da BBC Berify ta zanta da su sun ce akwai alamun Isra’ila ta aikata laifukan yaki.
Eitan Diamond – wani babban lauya da ke aiki a cibiyar agaji ta Diakonia International Humanitarian Law Centre da ke Jerusalem – ya ce akwai ‘yar hujja da ta kafe da shi a cikin yarjejeniyar Geneba ta hudu.
“Dokokin duniya sun haramta wadannan mamayar da barnata kadarorin fararen hula a lokacin yaki, sai dai idan ya matukar zama dole,” in ji Mr Diamond said.
“Amma barnata kadarori saboda kawai zargin yiwuwar za a yi amfani da su a gaba ba ya cikin uzurin da aka tsara a yarjejeniyar.”
Farfesa Janina Dill, darakta a cibiyar shari’a da yaki ta Odford Institute for Ethics, Law & Armed Conflict ta ce kasar da ta yi mamayar dole ta killace wani yankin domin kare wasu mutane – wadda ta ce ba zai yiwu a yi amfani da karfin soji ba.”
Amma wasu masanan sun kare rundunar IDF.
Gine-gine da dama da IDF ta rusa sun zama kufai, “in ji Farfesa Eitan Shamir, darakta a cibiyar BESA Center For Strategic Studies da ke Isra’ila kuma tsohon jami’i a ma’aikatar tsare-tsare. Ya bayyana wa BBC Berify cewa gine-gine sun barazana ga masu komawa garuruwan su saboda za su iya rushewa a kowane lokaci”.
Haka kuma Farfesa Shamir ya ce akwai rashin tsari.
“Wuraren sun zama na yaki,” in ji shi. “Ko da ma IDF ta mamaye wurin, da zarar Isra’ila ta janye, mayakan suna komawa su dasa bama-bamai ko su boye a ciki.”
Babu alamar janyewa a yunkurin na rusau. Kafofin watsa labarai na Isra’ila sun ce IDF ta dauko manyan katafila da ake kira D9 daga Amurka.
Kuma sashen BBC na BBC Berify ya gano gomman tallata guraban aiki da aka watsa a zaurukan Facebook na ‘yan Isra’ila da ake neman ma’aikata da za su yi aikin rusau a Gaza, wadanda aka rika yadawa tun a watan Mayu.
Wasu rubuce-rubucen sun bayyana wuraren da za a yi aikin a Gaza kamar “yankin Philadelphi” da “yankin Morag” – duk a karkarshin IDF.
Da BBC Berify ya tuntubi wani dan kwangila, sai ya ce, “ka je (wasu maganganu) da kai da Gaza.”
Wani masani – Adil Hakue na tsangayar shari’a ta Rutgers – ya yi hasashen rushe-rushen IDF ba za su rasa nasaba ba da yunkurin kafa “yankin soji” da za ta “mamaye daga baya” ba.
Wasu masana kuma sun ce rusau din share fage ne domin kafa “cibiyar agaji” a Rafah – Shugaban cibiyar nazarin tsaro da tsare-tsare ta Institute for Strategy and Security da ke Jerusalem – ya ce watakila suna so ne su tursasa wa Falasdina barin zirin baki daya.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya taba bayyana wa a baya a wani taro da ‘yan majalisa cikin sirri cewa IDF za ta rusa gine-gine ne domin ya zama Falasdina ba su da wurin komawa”.
Amma a wajen ‘yan Gaza, matsala cebabb.a.
Moataz Yousef Ahmed Al-Absi daga Tel al-Sultan ya ce an mayar da gidansa kufai.
“na koma gidan ne kimanin shekara biyu kafin a fara yakin, inda nake tsammanin zan cigaba da rayuwa. Amma yanzu ya zama kufai,” in ji shi.
“Na rasa komai, yanzu ban san yadda zan yi ba.”
Kungiyoyin agaji sun bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza
Kungiyoyi agaji fiye da dari sun yi gargadin yaduwar mummunar yunwa a Gaza, inda mutane fiye da miliyan biyu ba su iya samun abinci.
Kungiyoyin sun ce a halin da ake ciki yanzu hatta ma’aikatansu su na fama da karancin abinci a Gaza.
Kungiyoyin agajin da suka fitar da rahoton mawuyacin halin da mutane ke ciki a Gaza sun hada da kungiyar likitoci ta kasa da kasa, da Sabe the Children da kuma Odfam.
Sun ce ma’aikatansu ba su da wani zabi illa su shiga layin neman agajin abinci tare da al’umma Gaza, wani abu da ke sanya su shiga yanayin da za a iya harbe su, saboda kokarin nema wa iyalansu abinci.
Sun bukaci a samar da tsarin rabon kayan agaji a Gaza ta hannun hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Isra’ila ta amsa cewa an samu raguwa da gagarumin rinjaye kan yawan kayan agaji da Falasdinawa ke samu, amma ta musanta cewa akwai yunwa a yankin.
Dr Graeme Groom babban likitan kashi ne a asibitin London, wanda kuma ya yi aiki a Gaza a watan jiya.
Ya ce: ”A kullum abokan aiki na aiko mani sako domin sanar da ni cewa babu abinci. Kwanaki biyu da suka wuce, wani babban jami’in mu ya shaida mani cewa babu abinci, kuma ko kadan babu, sai ya ce ai babu komai, asali ma cikin matsananciyar yunwa suke.”
Wani rahoton da ma’aikatar lafiya ta Hamas ta fitar ya ce mutane fiye da 30 suka mutu saboda tsananain yunwa a kanaki uku, lamarin da Isra’ila ta ce farfaganda ce kawai.
Kungiyoyin sun bukaci a gagauta kawo karshen yakin domin samun damar shigar da wadataccen abinci ga al’ummar Gaza.
Mun Ciro Wannan Rahoto Daga BBC Hausa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp