Leadership News Hausa:
2025-07-26@08:35:05 GMT

Fahimtar Sabon Tunani: Mene Ne Birnin Zamani Na Al’umma

Published: 25th, July 2025 GMT

Fahimtar Sabon Tunani: Mene Ne Birnin Zamani Na Al’umma

Birni ba dajin da aka gina da siminti ba, wuri ne da bil Adama da nau’o’in halittu suke zama a ciki. Kasar Sin ta fidda sabuwar shawarar gina “birnin zamani na al’umma”.

Kwanan baya, kasar Sin ta kira muhimmin taro mai nasaba da biranen kasa, inda aka amince birane suna da rayuwa, ganin yadda suke yin numfashi, da girma, da samun kyautatuwa da kansa.

Shi ya sa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fidda shawarar cewa, idan muna son gina biranen zamani na al’umma, ya kamata a mai da matukar hankali kan al’umma, wato a bauta wa al’umma, a dogara kan al’umma wajen gina birane. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici

Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali

Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin. A halin da ake ciki, ana ci gaba da kokarin da ake yi na cikin gida da waje na wanzar da tsagaita bude wuta da kare fararen hula.

Ana zaman dar dar a lardin Suwayda da ke kudu maso yammacin kasar Siriya, inda dakarun gwamnati ke ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin tun da safiyar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin ‘yan kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin.

Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun samu nasarar kwace iko da lardin, tare da kafa shingaye na kasa domin raba bangarorin da ke fada da juna bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Sun kuma hana wucewar daidaikun mutane da ayarin motocin sojoji a kusa da lardin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
  • Dangote Ya Ajiye Muƙamin Shugabancin Kamfaninsa Na Siminti
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah
  • An Amince Da Biranen Kasar Sin 9 A Matsayin Biranen Dausayi Na Kasa Da Kasa
  • Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda
  • Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
  • Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
  • Yawan Ma’aikata Ne Ya Hana Borno Fara Biyan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi – Zulum