Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Falasdinu A Birnin Tunis Fadar Mulkin Kasar Tunusiya
Published: 27th, July 2025 GMT
An gudanar da gagarumin tattaki a kasar Tunisiya domin nuna adawa da yunwar da aka kakaba wa al’ummar Falasdinu a Gaza
Masu zanga-zangar Tunusiya a wani gagarumin tattaki da suka gudanar a tsakiyar babban birnin kasar, sun tabbatar da goyon bayansu ga gwagwarmayar Falasdinawa tare da bayyana cewa shiru da duniya ta yi kan killace Gaza da aka shafe sama da kwanaki 140 ana yi, abu ne da ba za a amince da shi ba.
A ci gaba da nuna goyon baya ga yunkurin da kasashen duniya ke yi na yaki da yunwa a zirin Gaza da aka killace, al’ummar Tunisiya sun fito kan tituna suna gudanar da gagarumin jerin gwano, suna daga tutar kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya da kuma rera wakokin adawa da shirun Larabawa da na sauran kasashen duniya dangane da wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya ke ci gaba da yi, da rufe mashigin ruwa, da kuma hana kai kayan agajin sama da kwanaki 140.
Mohsen Nabti, kakakin jam’iyyar Popular Current, ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Mafi ƙanƙantan matakin da ya dace shi ne yanke duk wata alaka da yahudawan sahayoniyya, kuma mafi ƙanƙanta taimako ga al’ummar Falasdinu shi ne a ɗage killacewar da aka yi wa musu, sannan mafi ƙaramar hukunta ‘yan mamaya shi ne kauracewa kasuwanci da maƙiyan yahudawan sahayoniya.
Masu zanga-zangar a titin Habib Bourguiba da ke birnin Tunis sun yi ta rera taken nuna goyon baya ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da kuma yin kira da a ci gaba da matsin lambar al’ummomin duniya don tilasta wa makiya dakatar da kisan gillar da suke yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Sin Ya Karyata Amurka Game Da Batun Yankin Xinjiang Na Sin a Taron Kwamitin Sulhun MDD
Wakilin dindindin na kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Fu Cong, ya yi magana a wani taro na bude kofar Kwamitin Sulhu na MDD game da hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar hadin gwiwar kasashen Musulmi (OIC), inda ya karyata batun da wakiliyar Amurka ta yi game da yankin Xinjiang na Sin.
Fu Cong ya ce, Sin ta nuna adawa kwarai tare da kin amincewa da zargi mara tushe balle makama da wakiliyar Amurka ta yi game da Xinjiang. A halin yanzu jihar Xinjiang na cikin kwanciyar hankali, tana samun ci gaban tattalin arziki, al’umma suna rayuwa cikin kwanciyar hankali, kuma suna cikin mafi kyawun yanayin ci gaba a tarihi. Amma da gangan Amurka ke kokarin yayata batun Xinjiang da nufin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Sin da kuma hana ci gaban Sin, wanda karara ya bayyana gaskiyar nuna son rai kawai, da kuma kasancewa mai fuska biyu.
Fu Cong ya kuma bayyana cewa, a cikin shekaru shida da suka gabata, sama da kasashe 100, ciki har da kasashe masu bin addinin Musulunci da dama, sun nuna goyon bayansu ga madafun iko na Sin a kwamiti na uku na babban taron MDD da nuna adawa da siyasantar da batun kare hakkin dan Adam da kuma amfani da shi a matsayin hanyar tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashe. Wannan ya tona asirin makircin Amurka na “amfani da Xinjiang don hana ci gaban Sin”, kuma mugun nufinta na tayar da husuma a tsakanin kasashe ya ci tura. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp