Tsofaffin Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu Tare Da Bashi Shawarwari Kan Matsalolin Tsaro
Published: 27th, July 2025 GMT
Tsoffin gwamnoni da suka fara mulki a shekarar 1999, da ake kira “Class of ’99,” sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a, inda suka gabatar da shawarwari na aiki domin magance matsalolin tsaro, inganta tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi a fadin ƙasar.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion, ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, da wasu tsoffin gwamnoni da suka yi mulki tare da Shugaba Tinubu lokacin da yake Gwamnan Jihar Lagos.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar da ta ɗauki fiye da awa guda, Igbinedion ya bayyana cewa ziyarar tasu na da nufin yin wata ganawa da ɗan ajinsu kuma su tattauna hanyoyin da za a ciyar da ƙasa gaba.
“Mun zo ganin takwaranmu, wanda muka fara mulki tare a shekarar 1999, don tattauna batutuwan da ke da muhimmancii ga ƙasa. Mun tattauna kan batun tsaro, tattalin arziki, noma da samar da ayyukan yi. Shugaban ya nuna damuwa matuƙa kan waɗannan matsaloli, kuma ya karɓi shawarwarinmu da hannu biyu.” In ji shi.
Igbinedion ya jaddada cewa tsaro ya kamata ya kasance babban fifiko na gwamnati, domin ba za a samu ci gaba ba tare da zaman lafiya idan ba tsaro ba.
Game da batun ayyukan yi, tsohon gwamnan ya yi kira da a kafa masana’antu kanana (cottage industries) a kowace ƙaramar hukuma a matsayin hanyar dorewar rage rashin aikin yi da fatara.
“In har za ka ba mutum tallafi yau, me zai faru gobe? Mun roƙi Shugaban Ƙasa da ya kafa ƙanana masana’antu a faɗin ƙasa domin mutane su samu ayyukan yi.” In ji shi.
Tawagar ta yaba wa Shugaba Tinubu bisa maraba da shawarwari masu amfani, inda suka ce Shugaban Ƙasar ya tabbatar musu da cewa zai yi la’akari da duk wani tunani mai amfani da zai ciyar da ƙasa gaba.
“Shugaban Ƙasa ya tabbatar mana cewa ƙofofinsa a bude suke don tattaunawa da shawarwari masu amfani da za su inganta ƙasar nan.” In ji Igbinedion.
Wannan shi ne karo na biyu da tsoffin gwamnoni na 1999 ke ziyartar Shugaban Ƙasa Tinubu tun bayan hawansa mulki.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum.
Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu.
Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike“Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu.
“An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma dole ne ya gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.”
Anyanwu, ya kuma yaba da hukuncin kotu wanda ya soke babban taron jam’iyyar na ƙasa, inda ya bayyana cewa wannan nasara ce ga mambobin PDP baki ɗaya.
“Muna jinjina wa ɓangaren shari’a bisa wannan hukunci da ya nuna adawa da zalunci da rashin bin doka. Wannan nasara ce ga kowane ɗan jam’iyyar PDP,” in ji shi.
Sauran da aka dakatar sun haɗa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba; mataimakin shugaban jam’iyyar na Kudu, Taofeek Arapaja.
Akwai kuma sakataren kuɗi na ƙasa, Daniel Woyenguikoro; jagoran matasan jam’iyyar, Sulaiman Kadade da mataimakin sakataren jam’iyyar na ƙasa, Setonji Koshoedo.
Sanarwar Anyanwu, na zuwa ne bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da shi da wasu magoya bayan Wike, lamarin da ya ƙara ba tsananta rikicin shugabanci a jam’iyyar PDP.
Anyanwu, ya kuma sanar da naɗa Alhaji Abdulrahman Mohammed, mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban jam’iyyar.