An Yanke Hukuncin Kisa Kan Yan MKO A Nan Iran
Published: 27th, July 2025 GMT
Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi sani da munafukai.
Kamfanin dillancin larabann Tasnim na JMI ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa mutanen biyu Mahdi Hassani da Behrouz Ehsani, sun yi amfani da makamai wadanda suka hada da gurneti da kuma wasu ind suka kashe mutane fararin hula a dai dai lokacinda ake hargitsi a cikin kasar don tada hankalin mutane da kuma wargaza harkokin tsaro a cikin kasar.
Labarin ya kara da cewa an tabbatar da tare da wata shakka ba suna aiki tare da kungiyar ta MKO wadanda suke adawa da JMI tun ranar kafa ta.
Kungiyar MKO dai it ace babban kungiya wacce take adawa da JMI ta kuma kashe mata manya-manyan malaman addini a farkon nasarar juyinn juya halin musulunci a kasar. Sannan daga baya tare da taimakon gwamnatin kasar Iraki ta yaki JMI a warare da dama. Daga karshe ta maida cibiyarta zuwa kasashen turai da Amurka inda suke samun makudan kudade don kimar da JMI. MKO ta kashe mutanen iran akalla 17000 tun lokacin shekara 1979 ya zuwa yanzu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp