Aminiya:
2025-07-26@09:57:47 GMT

Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato

Published: 25th, July 2025 GMT

Dakarun Runduna ta 3 ta ‘Operation Safe Haven’ masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a Ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a.

An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo

A cewar rundunar, kawun yaron ne ya sayar da shi shekaru uku da suka wuce.

Rundunar ta ce, an kuɓutar da yaron ne bayan wani samame da sojoji suka kai a maɓoyar miyagun da ke a Ƙaramar hukumar Riyom.

Da yake bayyana yadda aka kuɓutar da yaron, Manjo Zhakom ya ce “a ranar 22 ga Yuli, 2025, sojoji sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a lokacin da suka kai samame a maɓoyar ‘yan ta’adda a yankin Riyom.

“Bincike ya nuna cewa, kawunsa ne ya siyar da yaron shekaru 3 da suka gabata, amma an miƙa yaron ga Kansila mai wakiltar mazaɓar Zamko na Ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato, wanda ake sa ran zai miƙa yaron ga danginsa,” in ji kakakin.

A wani labarin makamancin haka, rundunar ta ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka kai a Ƙaramar hukumar Wase da ke jihar.

Manjo Zhakom ya bayyana cewa, “Bisa ga sahihan bayanan sirri da suka gano, ‘yan bindiga ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 a kan titin Kampani  zuwa  Kombodoro a Ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, sojojin sun yi kwanton ɓauna a kan hanyoyin ’yan fashi da ke kusa da unguwar Jeb.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: a Ƙaramar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100

Wasu mazauna Ƙaramar Hukumar Gusau da ke Jihar Zamfara, sun yi zanga-zangar lumana tare da neman gwamnati ta ɗauki kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a yankin.

Zanga-zangar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Laraba.

Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram Ibn Khalid a Borno

Jama’a da dama sun halarci zanga-zangar; wasu a kan babura, wasu a cikin motoci, wasu kuma a ƙafa.

Kuma sun taru a ƙofar gidan gwamnatin Jihar da ke Gusau domin nuna damuwarsu.

Ƙauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka, da Fegin Mahe.

Mazauna yankunan sun ce sama da mutum 100 ’yan bindiga suka kashe a baya-bayan nan.

Wani daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga ƙauyen Fegin Mahe, ya ce ’yan bindiga sun kashe ’yan uwansa da dama, sannan kuma sun sace musu kaya da darajarsu ta haura Naira miliyan ɗaya, ciki har da buhun taki guda 500.

Hare-haren sun hana manoma yin aiki a gonakinsu, saboda rashin tsaro a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Gusau, Abubakar Iman, ta bakin wakilinsa Aminu Wakili Mada, ya ce ya fahimci ƙorafin jama’ar yankunan.

Ya tabbatar da cewa gwamnati tare da jami’an tsaro suna aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, kuma za a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa wuraren da suka fi fama da matsala nan ba da jimawa ba.

Yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura domin bai amsa waya ba.

A wani labarin kuma, jami’an tsaro sun ceto mutum 11 da aka sace a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

An sace mutanen ne a ƙauyen Kaibaba da ke gundumar Turba a Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato.

An miƙa su ga Gwamnatin Jihar Sakkwato a ranar Laraba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matashi ya tono gawar kakarsa don yin tsafin kuɗi ya sare kan gawar kakarsa don yin tsafi
  • Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji
  • Duk da kashe jagororin ’yan bindiga, Turji na ci gaba da kai hare-hare
  • Wasu Mahara Sun Sake Kashe Mutum 14 A Wani Kauyen Jihar Filato
  • An kashe mata da yara a sabon harin Filato
  • Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan sama da mutum 100
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 95 a Neja, sun ceto mutum 138 da aka sace
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100