Faransa Ta Saki Dan GWagwarmayar Kasar Lebanon Goerge Abdullah Ya Bayan Zaman Kurkuku Na Shekaru 41
Published: 26th, July 2025 GMT
A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya.
Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.
Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya rage su, shi ne makamai.”
Akan mahaifarsa Gubyat, Goege Abdullah ya ce, a tsawon lokacin garin ya kasance wani alami na hadin kan al’ummar kasar.”
A filin saukar jiragen sama na “Rafiqul-Hariri” dake birnin Beirut, Goerge Ibrahim Abdullah ya sami kyakkyawar tarba daga ‘yan majalisa da jam’iyyun siyasa da kuma mutanen gari da dama.
A takaitaccen bayanin da ya yi a filin saukar jiragen saman na Beirut, ya sake tabbatar da matsayarsa na ci gaba da riko da gwgawarmaya da goyon bayan al’ummar Falasdinu.
Har ila yau ya ce; Matukar akwai gwagwarmaya, to da za a koma cikin kasa, sannan kuma ya ce; Gwagwarmaya tana nan da karfinta, ba ta yi rauni ba.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA