HKI Ta ce Ta Tsaida Yaki A Gaza Na Wani Lokaci
Published: 27th, July 2025 GMT
Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa.
Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Jarida Da Suka yi Shahada A Gaza Sun Kai 232, Yayin Da Wadanda Suka Rasa Rayukansu Sakamakon Yunwa Suka Kai 122
‘Yan jarida akalla 232 suka yi shahada sannan wasu 122 sun rasa rayukansu sabaoda masifar yunwa a yankin Zirin Gaza!
Yakin kisan kare dangi da ake yi a zirin Gaza yana ci gaba da lakume rayukan Falasdinawa da dama a kowace rana, manya da kanana…ta hanyar jefa bama-bamai, kisa, killace yankin da kakaba masifar yunwa.
A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu daruruwa, ciki har da masu neman agaji, sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ke dauke da ‘yan gudun hijira a unguwar al-Rimal da gidaje da sansanonin ‘yan gudun hijira a yankunan al-Amal, al-Tuffah, da al-Nasr, dake gabashi, arewacin Gaza.
Hakazalika an sha kai hare-hare ta sama a yankunan al-Balad da al-Amal da ke Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, da kuma harin bama-bamai da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila.