Tallafin Lafiya: Ƙungiyar Rotary Ta Raba Kayan Haihuwa kyauta Ga Mata Masu Juna Biyu A Kaduna
Published: 26th, July 2025 GMT
Ƙungiyar Rotary Club ta Kaduna Metropolitan ta raba kayan haihuwa fiye da 70 ga mata masu juna biyu a cibiyar kiwon lafiya ta Mando, Afaka.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban Rotary Club na Kaduna Metropolitan kuma shugaban Rotary Action Group for Peace, Rotarian Luqman Babatunde, ya jaddada cewa kayan haihuwar ba na siyarwa ba ne, kyauta ce don tallafa wa mata masu juna biyu musamman marasa ƙarfi.
Ya ce wannan tallafin ana gudanar da shi ne a wurare daban-daban a jihar Kaduna, yana mai jaddada cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya yin komai ba, shi ya sa ake buƙatar goyon bayan ƙungiyoyin sa-kai da na taimakon jama’a irin su Rotary.
Ya bayyana cewa wannan shirin ya samu ne ta haɗin gwiwa da kamfanin MotherCat, wanda ke kusa da cibiyar lafiya, don tunawa da watan kula da lafiyar uwa da jarirai.
Ya shawarci matan da su yi amfani da kayan yadda ya kamata tare da tunatar da su taken Rotary, Service Above Self, yana mai ƙarfafa su su rika taimaka wa wasu idan dama ta samu.
Shi ma ya sake jan hankalin masu cin gajiyar su yi amfani da kayan cikin hikima.
Haka nan, gwamnan yankin Rotary Clubs, Rotarian Joy Okoro, wanda Rotarian Victor Majekodunmi ya wakilta, ya bayyana cewa mata da dama masu juna biyu waɗanda ba su da ƙarfin siyan kayan haihuwa kan haifi jarirai a gida cikin mawuyacin hali.
Ya jaddada cewa wannan kyauta ba ta gwamnati bace, an samo ta ne daga gudummawar kungiyoyi da mutane masu kishin jinƙai, yana mai roƙon matan su yi amfani da kayan yadda ya dace.
Ita kuma babban jinya ta cibiyar lafiya, Hajiya Murjanatu Ahmed Rabiu, ta koka kan yadda wasu mata masu juna biyu ke ɓoye kayan haihuwar da gwamnati ko kungiyoyin ci gaban al’umma suka ba su, domin su karɓi kuɗi daga mazajensu.
Ta yi gargadin cewa su daina wannan dabi’a, tana mai cewa an rubuta sunaye da lambobin wayar waɗanda suka amfana a yau, kuma idan ya zama dole za a sanar da mazajensu cewa matansu sun karɓi kayan haihuwa kyauta daga Rotary.
A sakon ta na musamman, shugabar Ƙungiyar Matan ‘Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ), Comrade Sahura Jibrin Maidoki, ta roƙi matan masu juna biyu su nuna kayan haihuwar ga mazajensu domin rage musu nauyin kuɗi da kuma bawa mazajen damar mayar da hankali kan wasu bukatu. Ta kuma yi gargadin cewa kada su sayar da magunguna da sauran kayan tsaftar da ke cikin kyautar.
Mata biyu da suka amfana, Salamatu Tijjani da Faith Tori, sun gode wa Rotary da abokan haɗin gwiwarta saboda kyautar, suka kuma yi alkawarin yin amfani da kayan yadda ya kamata.
Wasu daga cikin kayan da aka raba sun haɗa da magungunan mata masu juna biyu, jakunkuna, kayan tsafta, ‘pads’, da ‘diapers’ da sauransu.
Wannan shirin, wanda ya yi daidai da Watan Lafiyar Uwa da Jarirai na Rotary International, ya samu halartar shugaban Rotary Club na Kaduna Main, Rotarian Ahmad Tijjani, da sauran shugabannin ƙungiyar a Kaduna tare da abokan haɗin gwiwa ciki har da Mothercat da NAWOJ.
COV: Naomi Anzaku Ekele
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kyauta Raba Kayan Haihuwa Rotary Tallafin Lafiya Ƙungiyar
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe aƙalla mayakan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno.
Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin.
DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabalaA cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna.
“A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas, ciki har da Munzirs biyu (kwamandojin filin daga na ƙungiyar) da kuma Qaid ɗaya (shugaban sashe).
“An kashe Modu Dogo, Munzir daga Dogon Chukun, wani Munzir da ba a bayyana ba, da Abu Aisha, shugaban sashe (Qaid) daga Tumbun Mota,” in ji wata majiya.
Majiyar ta ƙara da cewa wasu mayaƙa da dama sun samu raunuka, musamman waɗanda suka tsere da ƙafa bayan sun yi watsi da babura 14 da sojojin suka ƙwato.