Iran Ta Cilla Tauraron Dan’adam Mai Suna Nahid-2 A Yau
Published: 25th, July 2025 GMT
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa kombon kasar Rasha a wannan cillawar ta isar da taurarin dan’adam da dama zuwa sararin samaniya.
Kafin haka dai wannan kumbon na kasar Rasha ya taba aika taurarin dan’adam na kasar Iran guda 3 wato Khayyam, Parsa -1 da kuma hudhod.
Manufar cilla Nahid -2 dai shi ne kyautata harkokin sadarwa na JMI a sararin samaniya. Kuma kamfanonin gina taurarin yan adama a cikin kasa ne suka hada kai don ganin ya kammala.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a sararin samaniya kasar Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Ta Ci Gaba Da Inganta Sinadarin Uranium
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya cewa; Za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a cikin kasar Iran, kuma kasar ba za ta yi watsi da wannan hakkin na al’ummar Iran ba.
A cikin bayanin da ya yi a gefen ziyarar da ya kai ga iyalan shahidan Laftanar Janar Baqiri, Araqchi ya kara da cewa; Ko da yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya bisa tsari mai ma’ana da inganci.
Ya kara da cewa: Iran ba ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen samun amincewar kasashe da a wasu lokutan suke nuna damuwa, a maimakon haka, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da bukatunta na mutunta hakkinta na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, ciki har da inganta harkokin makamashi.
Ya ci gaba da cewa: Tattaunawar da za a yi a gobe ci gaba ce ta wadancan shawarwarin da suka gabata, matsayar Iran a bayyane take, wajibi ne duniya ta san cewa ba a samu wani sauyi a matsayin kasar ba, kuma za ta himmatu wajen kare hakkin al’ummar Iran a fagen samar da makamashin nukiliya ta hanyar lumana, musamman batun inganta makamashin nukiliya.