HausaTv:
2025-07-26@10:02:41 GMT

Mutanen A Netherlands Suna Zaman Dirshen Saboda Gaza

Published: 25th, July 2025 GMT

Dubban mutane a kasar Netherlands sun fara zaman dirshen don nuna damuwarsu kan yadda al-amura suke kara tabarbarewa a gaza, inda hki take ci gaba da kissan Falasdinawa a gaza, suke kuma kashesu da yunwa.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran dubban mutane a kasar sun yi zaman dirshen a tashoshin jiragen kasa na biranen Amsterdam da wasu wurare.

A cikin birnin Amsterdam kadai mutane dubbai suna taru a tashar jiragen kasa ta tsakiyar birnin da da Rotterdam.

Wasu tashoshin jiragen kasa da suke zaman dirshen sun hada da Enschede, Groningen, Eindhoven, Amersfoort, Assen, and Den Bosch. Wasu kuma sun fito da tutocin Falasdinu don nuna goyon bayansu ga falasdinawan. Sannan wasu sun fito da tukwane, cokula da kwanukan abinda, don nuna alamun yadda HKI ta hana abinci shigowa Gaza na watanni. Wanda ya sa da dama daga cikinsu suke mutuwa.

Har’ila yau wasu sun fito zanga zanga a kan titunan kasar ta Netherlands. Wadannan zanga-zanga da zaman dirshen dai yana nuna irin yadda mutane a duk fadin duniya suke kara kin HKI.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza

Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza!

Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya. Wannan ya saba wa duk dokokin jin kai da ka’idoji, kuma abin takaici, lamarin yana da kara muni.

Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza, suna fuskantar shamaki da aka sanya a zirin Gaza, baya ga tsarin rabon da wata gidauniya mai suna Gazan Humanitarian Foundation ke gudanarwa, wanda ke zama tarkon mutuwa. Ya zuwa yanzu, fiye da mutane dubu sun mutu yayin da suke jiran abinci, haƙƙin duk mazauna cikin wannan mawuyacin yanayi.

Ta yi gargadin cewa matakan karancin abinci na ci gaba da tabarbarewa, inda ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba da kuma matukar damuwa. Adadin matsalolin rashin abinci mai gina jiki, musamman a tsakanin yara, yana nuna mummunar tabarbarewa a wannan fanni. Akalla yara 5,500 ‘yan kasa da shekaru biyar ne ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, ciki har da yara akalla 800 da ke cikin matsanancin hali na rashin abinci mai gina jiki, ma’ana suna fuskantar barazanar yunwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Miliyoyin Al’ummar Yemen Sun Fito Taron Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Falasdinawa
  • Shugaban Kasar Ukraine Ya Nuna Sha’awar Ganawa Da Shugaban Kasar Rasha
  • Faransa Zata Bayyana Amincewa Da Samuwar kasar falasdinu
  • An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7 a Imo
  • Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • Al’ummar Fegin Mahe Sun Yi Zanga-zanga Kan Kisan Jama’a Da ‘Yan Bindiga Ke Yi
  •  Fiye Da  Kungiyoyin 100 A Duniya Sun Yi Gargadi Akan Halin Yunwa Da HKi Ta Jefa Mutanen Gaza A Ciki
  • A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24