An Fara Zaman Jin Ra’ayoyin Jama’a Kan Sauya Kundin Tsarin Mulki A Kano
Published: 27th, July 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano.
Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.
Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar.
Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin matakin doka domin warware su. Cikin batutuwan da za a mayar da hankali a kansu akwai: Sauye-sauyen harkar zaɓe, gyara a fannin shari’a, gyaran kundin tsarin mulki, da gudanar da shari’u da tsare-tsarensu.
Sauran muhimman batutuwa sun haɗa da:Inganta ‘yancin ɗan adam, tabbatar da shigar mata a harkokin shugabanci, raba iko da haɓaka ci gaban ƙananan hukumomi, batutuwan tsaro da tsarin aikin ‘yan sanda, da sauransu.
Sanata Barau ya buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da ra’ayoyi da shawarwari, yana mai cewa: “Mun buɗe ƙofofinmu ga dukkan ra’ayoyi. Kwamitin ya kuduri aniyar sauraron dukkanin bangarori yadda yakamata.” In ji shi.
Ya jaddada cewa shiga cikin irin wannan tsari na jama’a muhimmin al’amari ne ga makomar ƙasa.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Dr. Wali Sani, ya wakilta, ya jaddada bukatar haɗin kai, adalci da daidaito. A cewarsa: “ya zama mu yi ayyukan da za su haɗa ƙasa, su inganta adalci da daidaito, su kuma haɓaka ci gaba da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya.”
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: kundin tsarin Sanata Barau
এছাড়াও পড়ুন:
Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp