Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
Published: 27th, July 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja.
A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10.
“Ina alfahari da ku, Nijeriya gaba ɗaya na alfahari da ku. Kun ɗaga martabar ƙasarmu, ku abin koyi ne a zamanin ku. Ina mika godiya ta musamman ga masu horar da tawagar,” in ji Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar. Shugaban ya kuma miƙa saƙon ban girma ga Rasheedat Ajibade da ta samu lambar gwarzon ‘yar wasa a gasar.
Yayin da yake zantawa da tawagar, Tinubu ya yi addu’ar dawowar su lafiya zuwa gida, yana cewa: “Ina fatan zaku iso lafiya, Allah ya saka muku da alheri.” A madadin tawagar, Rasheedat ta gode wa shugaban ƙasa bisa amincewa da biyan cikakken alawus na ‘yan wasan, tana mai tabbatar masa da cewa tawagar za ta ba da dukkan ƙoƙarinta wajen kawo kofin WAFCON zuwa Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA