VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace
Published: 27th, July 2025 GMT
Daraktan Gidajen Rediyon Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Ndace, ya bayyana cewa an kammala shirin fara watsa shirye-shirye da harshen Mandarin, wanda shi ne harshe a hukumance na ƙasar China. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai tare da tawagar VON ga Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai.
Ndace ya ce ƙara harshen Mandarin zai kawo yawan harsunan da VON ke amfani da su zuwa tara. A yanzu, hukumar na watsa shirye-shirye da Hausa, Igbo, Yarbanci, Fulfude, Turanci, Faransanci, Larabci da Swahili. Ya bayyana cewa dukkan kayan aiki da tsare-tsare sun kammala don fara aikin, da nufin tabbatar da ɗorewar wannan sabon shiri.
China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 11, Sun Rusa Sansanoni A Dajin SambisaA cewarsa, wannan shiri ya yi daidai da hangen nesa na shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ke fatan inganta dangantaka da China. Ya ƙara da cewa hakan zai tallafa wajen yaɗa sahihan labarai game da Nijeriya da China a duniya, tare da ƙarfafa musayar shirye-shirye da tunani tsakanin ƙasashen biyu.
Jakadan China, Yu Dunhai, ya ce wannan mataki zai zurfafa haɗin gwuiwar kafafen watsa labarai tsakanin ƙasashen biyu, bisa yarjejeniyar da aka cimma lokacin ziyarar shugaban Nijeriya zuwa China. Ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a dangantakar diflomasiyya da zai ƙarfafa musayar al’adu da fahimtar juna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: shirye shirye da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.