Sojojin Yemen Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Amurka Samfurin MQ9
Published: 1st, April 2025 GMT
Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib.
Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba kuma za mu yi taraddudin daukar dukkanin matakan kare kai ba, akan jiragen ruwan abokan gaba a nan gaba.
Kwanaki biyu da su ka gabata, sojojin Yemen sun kai wasu hare-hare akan jirgin dakon jiragen yaki na “Trauman’ da sauran jiragen yakin da suke ba shi kariya.
Sojojin na Yemen suna kuma ci gaba da kai wa HKI hare-hare da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami a karkashin taya Falasdinawa fada, da kuma yin kira da a kawo karshen takunkumin da aka kakaba musu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse.
Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta.
A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse.
Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da Bello Musa Gada, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Kazaure, sai Barrister Mustapha Habu a matsayin Sakatari kuma Lauya mai ba da shawara.
Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa an zaɓi waɗannan mutane ne bisa cancanta, ƙwarewa da kuma nagartar halayensu, yana mai kira gare su da su yi kokarin sauke nauyin da aka dora musu.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya ce an riga an mika musu takardun naɗi kuma sun shirya tsaf don fara aiki nan take.
A nasa bangaren, Muhammad Fa’iz ya gode wa Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu, tare da alƙawarin gudanar da aiki da ƙwazo da himma.
Usman Muhammad Zaria