An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe
Published: 25th, July 2025 GMT
Babbar Kotun Jiha a Gombe mai lamba ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum uku bisa laifin haɗa baki da kuma kisan kai.
Alƙalin kotun Mai shari’a Haruna Kereng ne ya jagoranci shari’ar, inda ya ce kotu ta sami Dauda Mohammed Abubakar (wanda aka fi sani da Agenda) da Kabiru Abubakar (Gwarei) da Ibrahim Suleiman da laifi a kan dukkanin tuhume-tuhumen da ake musu dangane da kisan Ibrahim Yahaya a unguwar Herwagana da ke Ƙaramar Hukumar Gombe a ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Kotun ta ji cewa, mutanen ukun sun kai wa Ibrahim Yahaya hari ɗauke da makamai masu haɗari kamar: takubba da wuƙa, inda suka kashe shi tare da jikkata wasu mutane biyu, wato Ahmed Abubakar da Muhammad Ahmed Lawan a lokacin harin.
Shari’ar ta fara tun ranar 17 ga watan Nuwamba, 2022, kuma an kammala ta a ranar Laraba, 24 ga Yuli, 2025.
Kereng ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da laifin da waɗanda ake tuhuma suka aikata, kamar yadda doka ta tanada a sashe na 97 da 221 na dokar laifuka, wanda ta tanadar da hukuncin kisa ga wanda aka same shi da laifin haɗa baki da kuma kisan kai.
Yayin da yake yanke hukunci, Mai sharia Kereng ya ce “Kowannen ku za a rataye shi a wuyansa har sai an tabbatar da mutuwarsa ta hanyar gwajin likita.”
Ya kara da cewa kotu ba ta da ikon rage hukuncin, don haka ba ta saurari roƙon sassauci ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
Al’ummar garin Dukku a Ƙaramar Hukumar Dukku ta Jihar Gombe sun koka kan mummunan halin hanyar da ta haɗa su da babban birnin jihar, tare da kira ga gwamnati da ta gaggauta gyaran ta.
A cewar direbobi, tafiyar Dukku zuwa Gombe wadda a da take ɗaukar mintuna 50 kacal, yanzu ta koma fiye da awa biyu saboda lalacewar hanyar, abin da ke jawo gajiya da takaici ga fasinjoji da masu tuƙi.
An fara gina hanyar Gombe-Dukku-Darazo ne tun a shekarun 1980, aka gyara ta a farkon shekarun 2000. Sai dai daga baya aka yi sakaci da ita duk da kasancewarta hanyar da matafiya daga jihohin Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Bauchi da wasu ke bi.
“Gyaran motoci na cinye mana kuɗi”Usman Abubakar, direba mai shekaru 45 da gogewar tuki na sama da shekaru 19, ya ce lalacewar hanyar na sa direbobi kashe kuɗi masu yawa wajen gyaran motoci.
Bida Poly ta sa sojoji kula da jarrabawar ɗalibai ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu“Gaskiya hanyar ta lalace matuƙa. A da tafiyar Dukku zuwa Gombe kan ɗauki mintuna 45, yanzu kuwa ko awa biyu ba ta isa ba. Rami ne a ko’ina, musamman daga Tongoyel zuwa Bojude da Bozonshulwa. Sau da dama idan ka fito da safe sai ka tarar da motoci sun tsaya cak a hanya. Shock absorber, gilashi da sauran sassan mota suna yawan lalacewa saboda ramukan hanyar,” in ji shi.
Ya ce a da ‘shock absorber’ na iya kaiwa shekara biyu kafin ya lalace, amma yanzu ko watanni uku bai yi ba sai ya karye. Hakazalika tsohon gilashi da ake siya ₦90,000 yanzu cikin sati biyu kawai sai ya fashe.
Usman ya kuma ce ya sha yin haɗura a hanyar cikin watanni biyu kacal, inda tayar motarsa ta fashe, ‘shock absorber’ ya karye, sannan kingpin ya lalace — duka sakamakon shiga ramuka.
Wani direba, Abubakar Hassan, ya ce lalacewar hanyar ta kai shi ga tunanin barin aikin tuƙi gaba ɗaya saboda asarar kuɗi.
“Idan ruwan sama ya sauka, tafiya sai ta koma tamkar azaba. Sau da dama motoci kan kwana a hanya saboda lalacewa,” in ji shi.
Fasinjoji sun bayyana ƙalubaleKabiru Zubairu, ɗaya daga cikin fasinjojin da ke yawan amfani da hanyar, ya ce, “A da tafiyar kilomita 72 kan ɗauki mintuna 45 zuwa 60, yanzu ta koma awa biyu. Idan na taso Dukku da karfe 7:00 na safe, yanzu sai mu isa bayan 9:00. Wannan na jawo mana jinkiri sosai.”
Wani fasinja, Abubakar Aliyu, ya ce mutane da dama sun daina zuwa Gombe saboda halin hanyar. “Idan ka yi tafiya sai jikinka ya yi ciwo. Wasu matasa kan zuba yashi a cikin ramuka, amma ruwan sama yana wanke shi,” in ji shi.
Muhimmancin hanyar — MasanaMai sharhi a harkokin jama’a, Sulaiman Sa’idu Liman, ya ce kusan kilomita 64 daga cikin 72 na hanyar Dukku zuwa Gombe sun lalace, kuma motoci yanzu ba sa iya wuce gudu na kilomita 20 a awa ɗaya.
“Hanyar na da muhimmanci ga tattalin arziki da walwalar al’umma. Ana jigilar kayan gona, kayayyakin lafiya da marasa lafiya ta wannan hanya zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) Gombe,” in ji shi.
Likita Aliyu Bashir kuwa ya ce lalacewar hanyar na haifar da matsaloli ga lafiyar jama’a, musamman ƙura da ke haddasa cutar asma, da kuma haɗarin haihuwa kafin lokaci ga mata masu juna biyu saboda girgizar mota.
Kungiyoyi da direbobi sun yi kiraShugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dukku (DCF), Muhammad Bala Hashidu, ya yi kira da a gaggauta gyaran hanyar gaba ɗaya.
Shi ma shugaban Kungiyar Direbobi ta NURTW a Dukku, Abdulhamid Hassan, ya ce kusan kowace rana ana samun aƙalla motoci 10 da ke lalacewa a kan hanyar, abin da ya rage musu kuɗin shiga.
Gwamnati ta magantuMai magana da yawun gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da takwarorinta na Arewa maso Gabas domin samun tallafin Gwamnatin Tarayya wajen gyaran hanyar.
“Kwanan nan gwamnonin yankin sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu inda suka roƙi a gyara muhimman hanyoyi ciki har da wannan. Domin hanya ta tarayya ce, gwamnatocin jihohi ba su da ikon gyaran ta kai tsaye. Amma gwamnoni sun dage wajen ganin an gyara ta,” in ji shi.