Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja.

A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10.

Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya.

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda

“Ina alfahari da ku, Nijeriya gaba ɗaya na alfahari da ku. Kun ɗaga martabar ƙasarmu, ku abin koyi ne a zamanin ku. Ina mika godiya ta musamman ga masu horar da tawagar,” in ji Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar. Shugaban ya kuma miƙa saƙon ban girma ga Rasheedat Ajibade da ta samu lambar gwarzon ‘yar wasa a gasar.

Yayin da yake zantawa da tawagar, Tinubu ya yi addu’ar dawowar su lafiya zuwa gida, yana cewa: “Ina fatan zaku iso lafiya, Allah ya saka muku da alheri.” A madadin tawagar, Rasheedat ta gode wa shugaban ƙasa bisa amincewa da biyan cikakken alawus na ‘yan wasan, tana mai tabbatar masa da cewa tawagar za ta ba da dukkan ƙoƙarinta wajen kawo kofin WAFCON zuwa Abuja.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa da tsaki a Jihar Kano.

Gwamnatin Yobe ta bada tallafi ga iyalan ’yan banga da suka rasu Hulk Hogan ya mutu yana da shekara 71

A cewarsam Tinubu ya yi watsi da halin da yankin arewacin ƙasar ke ciki wajen gina Kudancin Najeriya da kuma samar musu da kayan more rayuwa.

“Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023, ya zargi jam’iyyar APC da karkatar da albarkatun ƙasa tsakanin ɓangarori biyu na Nijeriya.

Ya ce: “Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi,” in ji Kwankwaso.

Ya ce wannan ya sa ake fama da rashin tsaro da talauci da sauransu.

Kwankwaso ya ce yawancin hanyoyi da ke Arewacin suna cikin mawuyacin hali, wasu ma sun lalace, yayin da gwamnatin APC ke ci gaba da ware maƙudan kuɗaɗe wa ɓangaren ayyukan more rayuwa a Kudancin ƙasar.

Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sauya alƙibla domin tafiya da kowa da kuma tabbatar da cewa an raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata domin ci gaban dukkan sassan ƙasar.

“Yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnati ta kawo sauyi, domin mu san cewa ba gwamnati ce kaɗai ta wani ɓangare guda ba,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
  • Super Falcons ta lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko
  • Super Falcons sun lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko
  • Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
  • Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Na Mata 
  • Tsofaffin Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu Tare Da Bashi Shawarwari Kan Matsalolin Tsaro
  • WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe
  • Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Ware Arewacin Nijeriya A Rabon Arzikin Ƙasa
  • Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso