Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare
Published: 26th, July 2025 GMT
“Dole ne kasar nan ta samar da wata sabuwar hanya, domin samar da Kifin da zai wadace ta, wanda hakan zai kuma taimaka matuka wajen rage dogaro da shigo da Kifin daga kasashen waje da kuma kara habaka fannin” in ji Ministan.
Oyetola ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta himmatu kwarai da gaske wajen bai wa fannin goyon bayan da ya dace, musamman ta hanyar yin amfani da tsarin kimiyyar fasahar zamani da kuma zuba makudan kudade a fannin.
Kazalika, ya jaddada cewa; gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen ganin ana samar da wadataccen Kifi a kasar, musamman domin rage dogaro a kan wadanda ake shigowa da su daga kasashen ketare, duba da cewa; fannin na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa tattalin azikin kasar.
Kungiyoyiyon da suka halarci ganawar sun hada; manya-manyan masu ruwa da tsaki a fannin na kamun Kifi, kungiyar masu kamun Kifi ta kasa (FCFN), kungiyar masu kama dabbobin ruwa (TADAN), kungiyar masu kiwon Tarwada ta kasa (CAFAN) da sauran makamantansu.
Babban mai bai wa ministan shawara a fanin yada labarai, Bolaji Akinola, a cikin sanwar da ya bayar; bayan kammala taron ya bayyana cewa; Oyetola ya shaida wa mahalartan cewa, ma’aikatar na kara yin kokari wajen tallafa wa mata da matasa da suka rungumi sana’ar yin kiwon Kifi a karkashin shirye-shiyen da ma’aikatar ta kirkiro.
A cewar ministan, wannan shiri ne na tallafa wa mata da matasa; wanda kuma ya hada da tallafa musu da rance da kayan aiki, musaman don kara musu kwarin gwiwa, domin bayar da tasu gudunmawar wajen kara bunkasa fannin a Nijeriya, wanda kuma ya yi daidai na shirin Shugaban Kasa Bola Tinubu (Renewed Hope Agenda).
“Kara yawan matasan da za su rungumi sana’ar kiwon Kifi, wani babban maki ne, na kara samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa, wanda hakan zai kuma kasance wani mataki ne na rage marasa yin aiki a kasar” a cewar Oyetola.
“Mun mayar da hankali wajen tabatar da cewa, ba a bar mata da matasan kasar nan a baya ba, musamman don ganin an inganta rayuwarsu”, in ji Ministan.
A wajen ganawar, masu ruwa da tsaki a fannnin; sun kuma bijiro da wasu kalubale da ke ci gaba da ci wa fannin tuwo a kwarya.
A cewarsu, kalubalen sun hada da; yawan kamun Kifayen a Kogi, rashin samun rance, karancin kayan adana Kifin da ake adana Kifin bayan kamo su.
Sauran su ne, tsadar abincin da ake ciyar da su, wadanda ake shigo wa da su daga ketare, matsalar safararsu, karbar haraji barkatai, wanda ke sanyawa matasa ba sa iya shiga cikin sana’ar.
Sai dai, Oyetola ya bai wa masu ruwa da tsakin tabbacin cewa, wadannan kalubale da suka bijro da su, ma’aikatar za ta lalubo da mafita a kansu.
A cewarsa, a yanzu ana kan tattaunawa da Bankin Duniya, musamman domin a samu rancen kudi don tallafa wa masu kiwon Kifin a kasa tare da kuma samar musu da Inshora.
Ministan ya ci gaba da cewa, wannan zai kara tabbatar da nasarar da aka samu a shirin zamani na kamun dabbobin ruwa a Dam din Oyan da kuma sauran yankunan da ma’aikatar tasa ta yi hadaka da ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da sauran hukumomin gwamnatin tarayya.
“Wannan ganawa, ba iya nan za ta tsaya ba; amma tamkar yanzu ne aka fara ta, domin za a ci gaba da tattaunawa kan yadda za a ci gaba da habaka fannin,” in ji shi.
Shi kuwa a nasa jawabin, Wellington Omoragbon, Daraktan kula da kamun Kifi da sauran dabbobin ruwa, ya sanar da muhimmancin bukatar kara karfafa hadaka, domin jawo masu son zuba hannun jari a fannin, musamman domin a kara samar da wadataccen Kifi a fadin kasar baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran: Iran Tana Cikin Kasashe Biyar Na Duniya Da Suka Ci Gaba Wajen Kiwon Dabbobi
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi.
Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono ta hanyar kyautata da kula da lafiyarsu, domin rage dogaro da waje samar da nama da kuma nono.”
Haka nan kuma ministan na noma ya kara da cewa; Kara yawan dabbobin da ake samarwa a cikin gida,wata lalura ce ta tattalin arziki, da kuma kishin kasa.
Ministan Noma na Iran ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tasu tana kokarin ganin mayar da Iran zama cibiyar samar da abinci mafi girma a cikin wannan yankin.