Yayin da gasar wasannin kasa da kasa ta shekarar 2025 ke karatowa, an gudanar da bikin karba, da kaddamar da fitilar gasar a Asabar din nan, a shahararren gidan adana kayan tarihi na Sanxingdui, dake birnin Chengdu na kasar Sin.

Kaddamar da fitilar gasar a yau, ya alamta fara kidayar kwanaki 12, gabanin bude gasar karo na 12, wadda za ta gudana tsakanin ranakun 7 zuwa 17 ga watan Agusta dake tafe.

An tsara kewayawa da fitilar tsawon kilomita 11, a yankunan biranen Chengdu, da Deyang, da Meishan, kuma mutane 120 za su yi karba-karbar kewayawa da ita, wanda hakan ke alamta ruhin gasar da kyakkyawan zumuncin da take kullawa.

An ayyana ‘yar wasan motsa jiki Huang Zhangjiayang daga birnin Chengdu, wadda ta taimakawa kasar Sin lashe lambar zinari a wasan nuna fasahohin lankwasa jiki yayin gasar Olympics ta lokacin zafi a birnin Paris, a shekarar bara, a matsayin wadda za ta fara zagayawa da fitilar. Yayin da kwararren dan wasan kwallon tebur na kasar Sin Ma Long, zai kasance na karshe da zai kewaya da fitilar. An baiwa Ma Long wannan dama ne bisa kwarewarsa, da kuma nasarori masu yawa da ya cimma, a gasannin da ya wakilci kasar Sin a cikinsu. (Saminu Alhassan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da Shugaban Eritrea Isaias Afwerki domin tattauna halin da ake ciki a yankin,  Shugaba al-Sisi ya tabbatar da jajircewar Masar wajen tallafawa ‘yancin kai da kuma ‘yancin yankin Eritrea.

A yayin taron, wanda Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty da takwaransa na Eritrea, Osman Saleh Mohammed suka halarta, shugabannin biyu sun tattauna halin da ake ciki a yankin.

Sun tabbatar da hangen nesansu kan hanyoyin kawo karshen yakin a Sudan, suna masu  jaddada bukatar tallafawa cibiyoyin gwamnati na kasa, musamman Sojojin Sudan, tare da kin amincewa da duk wani yunkuri na kafa hukumomi ko cibiyoyi  masu kishiyantar gwamnati a kasar.

Shugaba al-Sisi ya jaddada matsayar Masar da kuma  kokarin da take yi  don kawo karshen yakin da kuma rage wahalhalun jin kai na al’ummar Sudan, ta hanyar yin aiki tare da abokan huldar Masar  don tabbatar da hadin kan Sudan, mutuncin yankin, da kuma ‘yancin kan kasa.

A nasa bangaren, Shugaba Afwerki ya nuna matukar godiyarsa ga rawar da y ace Masar tana  takawa karkashin jagorancin Shugaba El-Sisi, wajen karfafa zaman lafiya da kuma kokarin ci gaban  yankin kusurwar Afirka da Gabashin Afirka. Ya yi maraba da fadada hadin gwiwar tattalin arziki da Masar da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kan batutuwan kasa da kasa da na yanki masu amfani ga junansu.

Taron ya kuma yi magana kan sabbin abubuwan da suka faru a Somaliya, inda Shugabannin biyu sun jaddada kudurin kasashensu na amincewa da sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a taron kolin Masar, Eritrea, da Somaliya a Asmara a watan Oktoban 2014, wanda ya tabbatar da wajibcin girmama ka’idoji da dokokin kasa da kasa, musamman ma cikakken yankin Somaliya da dukkan kasashen yankin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
  • Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti