Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Furuci Da Halakar Sojan Guda Da Ya Jikkata A Zirin Gaza
Published: 27th, July 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila sun yi furuci da halakar daya daga cikin sojojinsu sakamakon raunukan da ya samu a Zirin Gaza
Majiyar sojojin mamayar Isra’ila ta tabbatar a ranar Asabar din da ta gabata cewa: Wani soja ya mutu sakamakon raunukan da ya samu kwanakin baya -bayan nan sakamakon tashin bam a kan hanyar wata motar soji a zirin Gaza.
Tun da farko, sojojin mamayar Isra’ila sun amince da mutuwar Sajan Reserve Vladimir Loza, mai shekaru 36, daga matsugunin Ashkelon.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan gwagwarmayar Falastinawa ke ci gaba da kai hare-hare da kuma kwantan bauna kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a fagage da dama a zirin Gaza, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da na dukiyoyi ga ‘yan mamayar.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas ta bayyana a ta bakin kakakinta, Abu Obeida, cewa: Dabarunta a wannan mataki ita ce ta “kokarin halaka makiya, da gudanar da hare-hare masu inganci, da kuma neman kame sojoji a matsayin fursunonin yaki.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp