Gaza: Ana Ci Gaba Da Samun Shahidai Da Yunwa Take Kashewa A Gaza
Published: 26th, July 2025 GMT
A daidai lokacin da aka cika kwanaki 659 daga fara kisan kiyashin Gaza, sojojin Sahayoniya suna ci gaba da killace yankin da hana shigar da abinci da magani.
Ma’aiktar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa ya zuwa wannan lokacin jumillar wadanda yunwa ta kashe sun kai 122 daga cikinsu da akwai kananan yara 83.
Da jijjifin safiyar yau Asabar, majiyar asibitin “Nasr’ ta sanar da cewa wata jaririya ta yi shahada saboda rashin abinci mai gina jiki. Haka nan kuma ta ce, jaririyar ‘yar watanni 6 da haihuwa ta yi shahada ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma magani saboda takunkumin da HKI ta kakabawa yankin na Gaza.
Babban jami’iin gudanarwa na ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza Dr. Munir al-Bursh ya sanar da cewa; Ana kara samun masu mutuwa saboda yunwa, musamman ma dai a tsakanin kananan yara.
Al-Bursh ya fada wa tashar talabijin din al-jazira cewa; Yunwa saboda rashin abinci da kuma rashin Magani ya sa jariran da suke cikin mata 3,000 sun mutu.
Haka nan kuma ya nuna mamakinsa akan yadda duniya ta gajiya wajen iya shigar da madarar jarirai cikin yankin Gaza domin ceto da rayuwar kananan yara da jarirai.
A wannan tsakanin ne dai Asusun kananan yara na MDD ( Unicef) ya yi gargadi akan mummunan halin da yaran Gaza suke ci gaba da shiga saboda rashin abinci mai gina jiki.
Ita kuwa shugabar hukumar Agaji ta kasa da kasa “Rd Cross” ta yi kira ne da a kawo karshen wahalhalu da bala’in da aka jefa mutane a Gaza, cikin gaggawa ba tare da ba ta lokaci ba.
A wani labarin na daban, kafafen watsa labarun HKI sun ce, sojojin Sahayoniya sun lalata tarin abinci mai yawa da aka ware domin shigar da shi zuwa yankin Gaza.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: saboda rashin abinci kananan yara
এছাড়াও পড়ুন:
Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna
Fitacciyar mai girkin nan, Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta sake kafa tarihi a duniya ta hanyar girka tukunyar dafa-dukar shinkafa mafi girma bayan shafe awa takwas tana girkin.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wani saƙon taya murna da Kundin Bajinta na Guinness ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara ’Yan sanda sun sasanta rikicin asibitin AKTH da KEDCOHilda Baci dai ta dafa shinkafa dafa-duka mafi yawa a tarihi tare da sauran kayan haɗi da sunadaran ɗanɗano wadda nauyinta ya kai kilo 8,780 a yankin Victoria Island da ke Legas.
A shekarar 2023 Hilda mai shekaru 28 ta shiga Kundin Bajinta na Guiness World Record bayan shafe awa 93 da mintuna 11 tana girke-girken abinci iri-iri.
A wannan karon, Hilda ta girka ƙananan buhuna 200 na shinkafa wanda nauyinsu ya kai kilo 4,000 da katan 500 na tumatir da kilo 600 na albasa da sauran kayan haɗi.
An gudanar da zaman girkin a fili a cikin birnin kasuwanci na Legas, lamarin da ya ja hankalin ɗaruruwan masu kallo.
Dafa-dukar shinkafa wadda a wasu harsunan ake kira Jollof rice abinci ne da ake sha’awa sosai a yankin Yammacin Afirka, inda ƙasashe kamar Nijeriya, Ghana, Senegal, Kamaru, da Gambiya ke da’awar cewa su ne ke da mafi ƙwarewa a wurin girka ta.
A shekarar 2023, Hukumar Ilimi, Kimiyya, da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta amince da Senegal a matsayin wurin da wannan abinci na dafa-dukar shinkafa ta samo asali.