Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5
Published: 27th, July 2025 GMT
Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin shafin intanet, ya zuwa ranar 27 ga watan, jimillar kudin shigar da kasuwar fina-finai ta Sin ta samu a lokacin zafi na bana ya zarce yuan biliyan 5, kuma adadin masu kallon fina-finai a lokacin ya kai miliyan 129.
Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya ko kuma yakin duniya na biyu.
Daga cikinsu, za a fitar da manyan fina-finai guda uku dake kunshe da “Dakin daukar hoto na Nanjing” nan ba da jimawa ba. Wadannan ayyuka sun dogara ne kan hakikanin abubuwan da suka faru a tarihi, wadanda ke nuna yadda jama’ar kasar Sin suka yaki hare-haren na Japan ta bangarori daban-daban, da kuma nuna babban karfin ruhin yaki da hare-haren. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yaki da hare haren
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta ce Ta Tsaida Yaki A Gaza Na Wani Lokaci
Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa.
Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa. Don hki ba abar amincewa bace. Tun shekara ta 2023 ne HKI ta kara tsananta hana shigo da abinci gaza.