Miliyoyin Al’ummar Yemen Sun Fito Taron Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Falasdinawa
Published: 26th, July 2025 GMT
Al’ummar kasar Yemen suna ci gaba da nuna goyon bayansu ga Gaza, miliyoyin mutane suka jaddada kiran zafafa kai hare-haren daukan fansa kan ‘yan sahayoniyya
Dubun dubatan jama’ar kasar Yemen ne suka fito kan tituna a jiya Juma’a a dandalin Al-Sab’en da ke tsakiyar fadar mulkin kasar Sanaa, da kuma dandali da dama a duk fadin sauran jahohin kasar, domin nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar al’ummar Gaza, kuma a matsayin wa’adi na shugabancin kasar Yemen, wanda ya sha alwashin daukar wasu zabukan kara kaimi wajen nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
Yemen ta ga wata rana ta musamman tare da jama’a da ba a taba ganin irinsu ba, suna amsa kiran Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi tare da nuna girman bala’in da ke faruwa a Gaza, da suka hada da kisa, kakaba yunwa, da kuma killacewa. Yamanawa sun amsa kiran tare da taron jama’arsu, da rera wakoki, da cikakkiyar shirinsu na sadaukarwa ga duk wani zaɓi na haɓaka ayyukan soji.
Ministan yada labaran kasar Yemen Hashem Sharaf al-Din ya ce, “Gaza ta yi kira, sannan Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya yi kira, kuma al’ummar Yemen sun mayar da martani ta hanyar zanga-zangar da ba a taba ganin irinta ba. Suna da yakinin cewa wannan gagarumin zanga-zangar za ta haifar da karuwar ayyukan soji da karin zabin da Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya yi magana akai, don haka wajibi ne makiya su yi la’akari da wannan gagarumin zanga-zangar.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC kuma Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, ya bayyana cewa Gwamnonin APC sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar gwamnati da ke Abuja.
Da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa bayan kammala taron, Gwamna Uzodimma ya bayyana ganawar da cewa “tattaunawa ce mai muhimmanci da Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta ikon ta na samar da nagartaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya”.
Ya ƙara da cewa, a matsayin su na gwamnoni, sun haɗu da Shugaban Ƙasa domin daidaita matsayin al’amuran jam’iyya da kuma muhimman abubuwan da suka shafi shugabanci.
Da aka tambaye shi ko ana sa ran yanke wasu manyan shawarwari ko takaddama a yayin Taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC da za a gudanar a gobe Alhamis, gwamnan ya ce, “Ba za mu iya cewa komai yanzu ba har sai mun isa wurin taron gobe.”
Ana sa ran taron na gobe Alhamis 24 ga watan Yulin 2025 zai tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jam’iyyar da kuma tsara hanyoyin ci gaba da haɗin kai da inganci a harkokin ta.
Bello Wakili