Gwamnati: Najeriya Ta Yi Asarar Tiriliyoyin Naira Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba
Published: 8th, March 2025 GMT
Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi.
Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan harkokin satar ma’adinai.
A cewar gwamnatin, cikin wadanda aka kama 320, kusan mutum 150 a halin yanzu suna fuskantar shari’a kuma wasu guda tara an dauresu, inda su kuma mutum hudu ‘yan kasar wajen aka dauresu a gidan yari.
Ministan bunkasa albarkatun kasa, Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartarwa na tarayya (FEC) wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
Ministan ya kuma ce, gwamnatin tarayya ta fuskanci kalubale wajen shawo kan matsalar hako zinari, musamman a arewacin Nijeriya, saboda al’adu.
Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai.
A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Jam’iyyar Adawa A Burtaniya Ya Ce HKI Tana Yaki A Gaza Ne A Madadin Gwamnatin Kasar
Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne.
Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Sky News dake birnin London a jiya Lahadi.
A lokacinda aka tambaye shi idan ya yarda da maganar Banyamin natanyaho kan cewa hamas yan ta’adda ce, kuma yana kokarin kwace gaza da shafi yan ta’adda ne, sai shugaban Conservative ya ce banzo nan don binciken kalmomin Natanyahu ba. Abinda nake son bada sanarwansa shi ne HKI tana yaki ne a madadin gwamnatin kasar Burtaniya, kamar yadda kasar Ukraine take yakar kasar Rasha a madadin kasashen turai.
Banda haka gwamnatin ta ki ta aibata HKI sannan bata yarda cewa cewa tana aikata kissan kiyashe ne a gaza ba.
Shugaban conservative yana fadar haka ne bayanda shugabannin kasashen Faransa, Burtaniya da kuma Canada suka bukaci HKI ta dakatar da kissan kiyashi na gaza ta kuma bar kayakin agaji su shiga yankin idan ba haka ba suna iya daukar matakai masu tsauri a kanta. Badenoch Shugaban jam’iyyar Conservative ya ce wannan bai wadatar ba.