Leadership News Hausa:
2025-06-16@13:57:11 GMT

‘Yan Bindiga Sun Sace Magidanci Da Iyalansa Da Makwabta A Abuja

Published: 27th, January 2025 GMT

‘Yan Bindiga Sun Sace Magidanci Da Iyalansa Da Makwabta A Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum da matarsa da dansa da wasu mutane biyu a Bwari da ke babban birnin tarayya, Abuja (FCT). LEADERSHIP ta tattaro cewa, an kai harin ne a unguwar Chikakore da ke Kubwa da misalin karfe 12 na safiyar ranar Litinin. Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon Tinubu Ya Isa Tanzania Don Halartar Taron Makon Makamashi Na Afrika  Majiyoyi sun ce, kimanin mahara 30 ne dauke da bindigogi kirar AK-47, suka kai hari gidan wani Mista Adefija Michael Akinropo, inda suka yi awon gaba da shi, da matarsa, da dansa, da kuma kanensa.

Bugu da kari, ‘yan bindigar sun afka makwabta kusa da wani gidan kiwon kaji, inda suka yi garkuwa da wani mutum tare da raunata matarsa ​​a yayin harin. Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansandan FCT, Josephine Adeh, ta bayyana cewa, za ta yi cikakken bayani bayan ta tattara bayanai kan lamarin.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Arakci: Babu Wani Dalili Na Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda ya tattauna ta wayar tarho da jami’ar harkokin waje ta tarayyar turai ya bayyana cewa, ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ba shi da wata ma’ana, kamata ya yi jami’an tarayyar turai din su yi Allawadai da wuce gona da irin HKI akan Iran.

Da safiyar yau Asabar ne dai jami’ar diplomasiyyar ta turai Kaja Kallas ta kira yi minsitan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci inda su ka tattauna halin da ake ciki a yammacin Asiya da ya hada da harin da HKI ta kawo wa Iran.

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana harin na HKI da cewa, wuce gona da iri ne da keta hurumin kasar Iran, kuma harin da ta kai wa cibiyoyin Nukiliya ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da su ka hada da malaman jami’oi , da kuma mata da kananan yara.

Ministan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi Allawadai da abinda HKI ta yi na take dokokin kasa da kasa.

Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi ishara da cewa, kudurin da majalisar alkalai ta hukumar makamashin Nukiliyar Iran ta fitar akan Iran wanda kuma kasashe uku na turai tare da Amurka su ka gabatar da shi, shi ne ya bude wa ‘yan Sahayoniya mashigar da su ka yi amfani da ita wajen wuce gona da iri akan Iran.

A nata gefen babbar jami’ar diplomasiyyar tarayyar turai ta bayyana rashin jin dadinta akan abinda yake faruwa a cikin yankin na yammacin Asiya na rikice-rikice, tare da bayyana cewa suna goyon bayan aiki da diplomasiyya domin tabbatar da zaman lafiya.

A wani labarin mai alaka da wannan kasar Oman ta sanar da cewa, ba za a yi taron da aka shirya yi a tsakanin Iran da Amruka ba.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ce ta fitar da sanarwar cewa; Tattaunawar da aka shirya cewa za a yi a tsakanin Amurka da Iran ba za a yi ta ba a gobe Lahadi.

Ministan harkokin wajen na Oman ya kara da cewa; Diplomasiyya ce kadai ya kamata ta zama hanyar cimma zaman lafiya mai dorewa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila
  • Martanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Ta’addancin ‘Yan Sahayoniyya ya Shiga Rana Ta Biyu
  • Trump ya dakatar da kamen baƙin haure a wasu wurare na Amurka
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 100 a Benuwe
  • Wutar lantarki ta kashe mutum 5, ta jikkata 13 a Gombe
  • Arakci: Babu Wani Dalili Na Ci Gaba Da Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka
  • Wutar Lantarki Mai Ƙarfi Ta Yi Ajalin Mutum Biyar A Gombe
  • Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai
  • An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu
  • Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8