Malaman Furanare 116 Sun Gabatar da Addu’o’i a Zaria
Published: 2nd, March 2025 GMT
Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu’o’i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna.
Malaman sun gudanar da addu’o’in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin Malaman yankin.
Sakatariyar ilimi ta karamar hukumar Zaria, Dr Hassana Lawal ta shedawa manema labaru lokacin addu’o’in a zaria cewa a kalla Malaman makarantun firamare 2,225 ne suka amfana da tallafin kayan abinci domin gudanar da azumin watan Ramadan.
A cewar ta,kayan abincin sun hada da kilo 25 na shinkafa da lita 4 na man gyada da fakitin tafiya da kuma kilo 10 na buhun garin samabita.
“Wannan shine karo na 8 da shugaban majalisar wakilan ya baiwa malaman makarantar firamaren irin wannan tallafin tun daga lokacin da hau karagar shugabancin majalisar.
“Baya ga tallafin kayan abinci,ya baiwa duk shugabannin makarantun firamare 116 da ke yankin kyautar babura domin saukaka masu zuwa wurin aiki,wanda a cewar ta abin godiya ne matuka”.
Haka kuma sakatariyar ilimin ta yaba da kokarin da gwamnan jihar kaduna, Malam Uba Sani ke yi na bunkasa ilimi a jihar.
Dr Lawal ta ce kokarin da gwamnan ke yi sun kushi gina ajujuwa 12 a makarantun firamare da dama a karamar hukumar Zaria baya ga tallafin kayan karatu, wanda hakan ne yasa dole su yi masu addu’o’in.
Ta kara da cewa Malaman sun zami watan Ramadan ne domin gudanar da addu’o’in Allah ya baiwa shugaban majalisar wakilai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi nasara da kwarin gwiwa wajen ci gaba da bunkasa ilimi a jihar.
A nashi jawabin, sakataren Kungiyar malamai na karamar hukumar Zaria, Malam Kasimu Mohammed ya ce tallafin kayan abincin ya taimaka wa Malaman matukar gaske.
A don haka sai ya bukaci sauran yan siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi shugaban majalisar wakilan ta hanyar tallafawa Malaman makarantun firamare a yankunan su.
Haliru Hamza
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Furame Zaria karamar hukumar Zaria makarantun firamare shugaban majalisar tallafin kayan
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, cikakken zama na 4 na kwamiti na 20 na JKS ya amince da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15. Sin za ta yi amfani da wannan damar don ci gaba da gyare-gyaren tattalin arzikinta, da kuma fadada bude kasuwancinta mai zurfi ga ketare, ta haka za ta ci gaba da ba da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik da sauran kasashen duniya ta hanyar zamanantar da al’ummarta. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA