An Kaddamar Da Taro Na 10 Na Zaunannen Kwamitin Majalisar CPPCC Karo Na 14
Published: 2nd, March 2025 GMT
An kaddamar da taro na 10 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a yau 1 ga watan Maris a nan birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar CPPCC Wang Huning ya halarci taron.
A gun taron, an zartas da kudurin gudanar da zama na 3 na majalisar CPPCC karo na 14 a ranar 4 ga wannan wata a birnin Beijing, an kuma gabatar da shawara kan ajendar zaman, wato sauraro da yin bincike kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC da yadda aka gudanar da ayyukan da aka cimma daidaito a kai, a gun zama na 2 na majalisar CPPCC karo na 14, da halartar zama na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, da kuma sauraro da tattaunawa kan aikin gwamnatin kasar da sauran rahotanni. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: CPPCC karo na 14 majalisar CPPCC
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Kolin JKS Ya Shirya Taron Bita Tare Da Wadanda Ba ’Yan Jam’iyyar Ba
Kwanan baya, kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya shirya taron bita tare da wadanda ba ’yan jam’iyyar ba, dangane da yanayin tattalin arzikin kasar, da kuma ayyukan tattalin arziki da za a aiwatar a rabin shekarar bana ta biyu, domin sauraren ra’ayoyinsu.
Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar ne ya shugabanci taron tare da ba da muhimmin jawabi, inda ya ce, dole ne a zage damtse wajen gudanar da ayyukan tattalin arziki a rabin shekarar bana ta biyu, kuma a tabbatar da gudanar da ayyukan ba tare da tangarda ba, kana a aiwatar da cikakken sabon tunanin raya kasa daga dukkan fannoni, da gaggauta kafa tsarin raya kasa, da kiyaye aiwatar da manufofi ba tare da matsala ba, da inganta aiwatar da manufofi tare da yin hangen nesa da sanin ya kamata.
Shugaban na Sin ya ce, ya zama wajabi a mayar da muhimmanci ga samar da guraben aikin yi, da kwantar da hankulan kamfanoni, da tafiyar da harkokin kasuwanci, da samar da tabbaci game da hasashen da ake yi kan tattalin arziki, da karfafa sayayya, da dakatar da yin takara maras dacewa, da kawar da cikas a kasuwar gida, da rungumar wani sabon tsarin ci gaba mai “zagaye biyu”, wato wanda zai tanadi amfani da kasuwar gida a matsayin jigo, tare da barin kasuwannin gida da na waje su karfafi junansu, a kokarin cimma manufar raya tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar kasar a bana, da samun nasarar kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp