2025-10-31@04:29:11 GMT
				 
				 إجمالي نتائج البحث: 4393
				 
                «Yammacin Kogin Jordan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
	Tawagar sun gabatar da kansu ga babban sakataren hukumar gudanarwar ci gaban Jihar Katsina, Dakta Mustapha Shehu. Tawagar sun ce ziyarar wani bangare ne na shirye-shiryen gudanar da aikace-aikace domin inganta zaman lafiya da kuma sanar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira.   Gwamnan Katsina ya yaba wa Bankin Duniya da ya yi hadin gwiwa da Jihar Katsina don fuskantar matsalolin tsaro da kuma tallafa wa ‘yan gudun hijira. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025  Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025  Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu...
	Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026.   Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki na zamia da kuma ci gaba da janyo hankalin masu son zuba hannun jari zuwa ga fannin, wanda hakan zai kuma kara sanya gasa a cikin wadanda suke a cikin fannin.   Ya bayyana cewa, masu son zuba hannun jari a fannin suna ci gaba da nuna shawarsau, musamman saboda sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinbu ta kirkiro da su, a fannin kara...
	  Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau? Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya. Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su...
 
	Kwamandan Dakarun Sa Kai Na Iran Ya Bayyana Cewa: Iran A Yayin Yaki Da Isra’ila Ta Tarwatsa Wasu Muhimman Wurare 21
	Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da tarwatsa wasu muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya a lokacin yakin 12 Kwamandan Dakarun sa-kai na Basij Birgediya Janar Gholamridha Sulaimani ya bayyana cewa: Tunanin kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin yakin kwanaki 12 da aka yi, wauta ce ta makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda suka gaza a yunkurin da suka yi. Ya jaddada cewa: Iran ta lalata muhimman wurare 21 na ‘yan sahayoniyya da makamanta masu linzami a yakin karshe. Birgediya Janar Gholamreza Soleimani ya bayyana a wurin taron tunawa da shahidai a Isfahan cewa: Makiya sun yi tunanin cewa za su iya kawar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran nan da kwanaki 10, kuma sun yi niyyar haifar da hargitsi da...
	Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka, inda ta gudanar da samame a wata maɓoya da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da safarar ƙwayoyi a cikin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa jami’an da ke ƙarƙashin Gombe Division ne suka gudanar da samamen da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ranar Alhamis 10 ga Oktoba, 2025. Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo A cewar sanarwar, jami’an sun kai samamen wata maɓoya da ke bayan jerin shagunan Ƙaramar hukumar Gombe, (Local Government Shopping Complex), inda ake zargin...
	Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta sanar da nadin CP Dantawaye Miller a matsayin sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja.  Ya karɓi ragamar aikin ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Oktoba, 2025, daga hannun CP Ajao Adewale, wanda Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, Kayode Egbetokun, ya sauya wa wajen aiki. Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, sabon kwamishinan ya bayyana cewa zai ci gaba da inganta tsaro tare da bunkasa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’ummar Abuja. Ta ce CP Miller ya yi alkawarin...
	Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar.   Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.   Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki...
	Abin da ya rage yanzu shi ne za a zuba ido don ganin irin sauyin da zai kawo na tsaro a birnin tarayyar, sakamakon taɓarɓarewar tsaro da ya addinin garin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025  Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025  Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025
	Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku. Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda hakan ya saba wa tsammanin wasu mambobin, musamman daga bangaren Obi. A cewar Bolaji, a halin yanzu ADC ba ta mai da hankali kan wane zai tsaya takara a karkashin tutan jam’iyyar ADC a zaben 2027 ba. “A halin yanzu dai, babu wanda aka tattaunawa kan cewa shi ne sahihin dan takara ko kuma za su gudanar da zaben fitar da gwani. Idan mun kai...
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima  October 17, 2025  Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025  Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 
	Majalisar koli ta sisaya ta kasar yamen ta sanar da nada major janaral Yousef hassan al-Madani a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin sojin na kasar Yamen , inda ya gaji Janaral Mohammad Abdulkarim Al-Ghumari wanda yayi shahada a baya bayan nan sakamakon Harin da sojojin HKI suka kaddamar kan kasar ta yamen. Wannan sabon nadi ya kara tabbatar da karfin guiwa game da jagoranci tsakanin dakarun sojin kasar Yamen a dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da gwagarmaya kan dakarun hadin guiwa da Saudiya ke jagoranta, kuma sun kara jaddada matsayarsu ta gwagwarmayar yanto dukkan yankunan dake karkashin yan mamaya ciki har da birnin Qudus, Janaral Ali Ghumari yana daya daga cikin mayan kwamandoji masu hazaka acikin dakarun...
	Baya ga yi masu afuwa, Shuagaba Tinubu, ya kuma karama su da lambar yabo ta kasa. ‘Yan Ogonin su tara, sun dai fuskanci shari’a ne, bisa zarginsu da kitsa kisan sarakunan Ogoni Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage da kuma Samuel Orage. Kotu ta tuhumi ‘yan Ogonin su tara, ta kuma yanke masu hukuncin rataya a ranar 10 ga watan Numambar 1995. Hukucin na Kotun, a wancan lokacin, ya haifar da hatsaniya tare da yin suka daga bangaren manyan shugabannin kasasshen duniya, daidaikun mutane da sauran kungiyoyi, musaman duba da cewa, an yanke masu hukuncin ne, a lokacin da ‘yan kasar ke nuna tsanar mulkin soji, biyo bayan soke zaben shugaban kasa, da ake da yakinin an yi sahihin zabe...
	Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, taron goron gayyata ne na kafa Nijeriya a matsayin cibiyar samar da makamashi tare da sabuntawa a Afirka, sannan kuma sauyin da aka samu na makamashi Nijeriya, ya bayar da damar zuba jari na sama da dala biliyan 410, daga tsakanin yanzu zuwa shekarar 2060. Ya kara da cewa, “Daga cikin wannan, ana kuma bukatar sama da Naira biliyan 23, domin fadada hanyoyin samar da makamashin da kuma hada miliyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda har yanzu suke rayuwa cikin matsalar wutar lantarki, amma yanzu babban burinmu shi ne, samar da tsarin samar da wutar lantarki mai karfin mega wat 277, nan da shekarar 2060. Cikar wannan buri, ya wuce batun zuba hannun jari kadai, domin...
	Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da...
	  Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.   Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.   Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen...
	A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara. Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa a yayin da hare-hare ke karuwa a duk shekara duk da karin kudaden tsaro da ake warewa.. A Sakkwato, kauyuka da dama kamar Giyawa, Kurawa, da Unguwar Lalle a gabascin Sakkwato hedikwatar gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji sun fuskanci hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a baya- bayan nan. A Karamar Hukumar Sabon- Birni, wasu mazauna yankin sun tsere domin tsira da...
	Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Israel Sunny-Goli, ya shawarci tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ya guji duk wata matsin lambar da wasu ƴan siyasa ke yi masa na ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Sunny-Goli ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin halartar shirin Politics Today na tashar Channels, inda yake mayar da martani kan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri, daga jam’iyyar PDP. Ya ce, “Ina ganin Jonathan zai karɓi wannan lamari da zuciya ɗaya saboda mutum ne mai son cigaban jiharsa. Duk da maganganun da ake yi kan zai tsaya takara, bana ina ganin zai yi kuskuren hakan saboda lokaci ya riga ya wuce.” Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya...
	 Shugaban kasar ta Sudan Janar Abdulfattah al-Burhan  ya ziyarci Masar inda ya gana da takwaransa Janar  al-Sisi, inda su ka tattauna halin da ake ciki a Sudan, da kuma matsalolin da yankin yake fuskanta. Haka nan kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi akan madatsar ruwan kasar Habasha da Masar take da sabani da Addis Ababa akai, da kuma yadda za a fuskanci wannan matsala. Kasar Sudan dai ta fada cikin yakin basasa ne tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023 wanda ya zuwa yanzu ya ci rayuka da dama da kuma mayar da wasu miliyan 14 zama ‘yan hijira. Shugabannin biyu na kasashen Masar da Sudan sun kuma tattauna daukar mataki na bai daya akan madatsar ruwan na kasar...
	A jiya Alhamis jiragen yakin HKI sun kai hare-hare na wuce gona da iri garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon da hakan ya yi sanadiyyar shahada da kuma jikkatar mutane da dama. Majiyar tsaro daga kudancin Lebanon ta ambaci cewa, mutum daya ya yi shahada yayin da wasu 7 su ka jikkata. Hare-haren sun shafi garin Kafar-Tabinet da kuma akan hanyar Kausariyyah al-siyadah. Haka nan kuma jiragen na ‘yan sahayoniya sun kai wasu hare-haren a garin Ansariyyah, da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar mutane 6. Hare-haren na HKI suna a karkashin keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label...
	Jaridar Wall Street Jouranl ta kasar Amurka ta buga labarin da yake cewa, kasar Amurka ta fada girke makamai a kusa da tekun Caribbean da kuma wasu jiragen sama a arewacin kasar Venezuela. Labarin ya kara da cewa;Rundunar da ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon” ta girke ta zaratan mayakan kundunbala ce wacce ta kashe Usama Bin Ladan a kasar Pakistan. Wani sashe na rundunar ya hada jirage masu Angulu da ake iya amfani da su wajen kai hari. A cikin kwanakin bayan nan dai Amurka ta kara matsin lamba akan kasar Venezuela ta hanyar kai wa jiragen ruwan da suke fitowa daga kasar hare-hare, bisa zargin cewa suna dauke da muggan kwayoyi zuwa Amurka. Gwamnatin Venezuela da kasashen yankin masu...
	A yammacin jiya Alhamis ne sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda ya isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ga shugaban na Rasha. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da huldar dake tsakanin kasashen biyu, da hadin gwiwar tattalin arziki, da ci gaban yankin, da kuma sauran batutuwa na kasa da kasa. A makon da ya gabata, Putin ya ce mahukuntan Isra’ila sun bukaci ya isar da sako ga Iran cewa ba su niyar sake kaddamar da wani hari a kan kasar ta Iran. “Muna ci gaba da samun sakonni daga jagorancin Isra’ila suna neman...
	Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis. Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da mambobin rundunar tsaro ta jihar Zamfara ke amsa kiran gaggawa daga kauyen Tungawa da ke ƙaramar hukumar Tsafe. An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC “Maganar da nake yanzu haka, an kwashe gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Gusau domin jana’iza,” in ji wani shaida da aka bayyana sunansa da Tsafe....
	  Ya ce kamar ko da yaushe, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan muhimmiyar rawar da FAO ke takawa a bangaren aikin gona da samar da abinci a duniya.   An kafa hukumar FAO ne a ranar 16 ga watan Oktoban shekara ta 1945, kuma Sin na daya daga cikin kasashe mambobi da suka kafa ta. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar? October 16, 2025  Daga Birnin Sin Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin October 16, 2025  Daga Birnin Sin Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da...
	  An dage ci gaba da binciken har sai ranar 20 ga wata. Maris na shekara mai zuwa, a makon da ya gabata, dubban mutane ne suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Manchester domin gudanar da jana’izar Hatton, wanda ya kasance shahararren dan wasan dambe a kasar Ingila.   Dan wasan gaban Oasis Liam Gallagher, tsohon dan wasan Ingila da Manchester United Wayne Rooney da kuma tsohon zakaran ajin masu nauyi na duniya Tyson Fury na daga cikin taurarin duniya na wasanni da suka halarci jana’izar Hatton. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc  October 15, 2025  Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14,...
	Sashen kashe radadi domin gudanar da aikin tiyata ga marasa lafia na asibitin gwamnatin tarayya FMC da ke garin Birnin Kudu a jihar Jigawa ya gudanar da bikin ranar bada maganin radadi ta duniya ta bana. Kungiyar ma’aikatan bada maganin kashe radadi dan yin aikin tiyata ta Duniya ce ta kebe ranar 16 ga wata Oktobar kowacce shekara domin bikin wannan rana. Shekaru 170 ke nan da fara amfani da maganin kashe radadi, inda wasu likitoci su ka yi gwajin wannan magani a asibitin birnin Massachusetts na kasar Amurka, abin da ya kawo sauyi wajen yi wa marasa Lafia aikin tiyata daga shekara 1846.  Malam Aliyu Umar Yusuf na sashen bada maganin kashe radadi na asibitin gwamnatin tarayya FMC...
	Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa wasika daga daukacin malamai da daliban jami’ar nazarin aikin gona ta kasar Sin, inda ya taya dukkan malamai da dalibai da ma’aikatan jami’ar, da kuma wadanda suka kammala karatu a jami’ar murnar cika shekaru 120 da kafuwar jami’ar. Xi ya yi fatan jami’ar za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, da kudurce aniyar inganta aikin gona don amfanin kasa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare kan hanyoyin koyarwa da ilmantarwa, da kara kokarin bincike, da kirkire-kirkire a fannin aikin gona, da kuma amfani da sakamakon binciken yadda ya kamata, ta yadda za a kai ga horar da karin kwararrun masana a fannin aikin gona, don ba da sabuwar gudummawa ga...
	Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka tsakanin kasashen musulmi a gabashin kasar Iran. Shugaban ya kara da cewa rikicin baya-bayan nan tsakanin Afghanistan da Pakistan ya haifar da damuwa sosai a tsakanin dukkanin kasashen yankin ciki har da Iran da ke da iyaka da kasashen biyu. Ya kara da cewa, Iran za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an rage zaman dar-dar, da inganta tattaunawa, da karfafa dankon zumunci a tsakanin...
	  “Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”   Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC October 16, 2025  Labarai Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku October 16, 2025  Manyan Labarai Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025
 
	Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi
	  Haka kuma, shugabar kasar Iceland Halla Tomasdottir ta ce, a matsayin wata babbar kasa, kiran da kasar Sin ta yi yana da muhimmanci ga sauran kasashen duniya. Ayyukan da kasar Sin ta yi a fannin tabbatar da ci gaban mata da daidaiton jinsi, sun kasance abin koyi ga kasashen duniya.   Bugu da kari, shugabar kasar Dominica Sylvanie Burton, ta ce jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin taron kolin mata na duniya, ya samar da sabon karfi ga raya ci gaban mata bisa dukkan fannoni, kuma kasarta na fatan ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Ɗaga...
	  Hichilema ya kuma jinjinawa kamfanonin Sin, bisa yadda suke inganta darajar albarkatun dake kasarsa ta hanyoyin zuba jari, kana ya godewa Sin bisa yadda ta bude kasuwanninta ga Zambia da ma sauran sassan nahiyar Afirka baki daya. (Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan October 15, 2025  Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji  October 15, 2025  Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025
	An fara tantancewar da misalin ƙarfe 12:55 na rana, inda ake sa ran Farfesa Amupitan zai gabatar da tarihinsa da kuma amsa tambayoyin da ‘yan majalisar za su yi masa, kafin yanke shawara kan tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban INEC. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 16, 2025  Manyan Labarai Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki October 16, 2025  Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October 16, 2025  Da ɗumi-ɗuminsa Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP October 15, 2025  Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025 
	Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama gungun mutane 11 da ake zargi da kasancewa ’yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Kano. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare hanyoyin zuwa Sha’iskawa-Charanchi da Katsina-Kankia-Kano, suna kwace dukiyoyin matafiya. DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi Ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Dikko Ma’aru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Ma’aru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir. Sauran sun haɗa da Abdullahi Zubairu, Muhammad...
	Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dorawa kasar ta bunkasa amfani da karfe ko a cikin gida sannan da wasu dabarbarun don saida su ga kasashen duniya. Labarin ya kara da cewa yawan karshen da ake samarwa a cikin gida ya karo da kasha 34% a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara ta 2025, sannan yawan karfen da iran take satarwa zuwa kasashen wajen ya...
	Majiyar hukumar fursinoni ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa masu gida a gidajen yarin HKI sun daki Marwan Barghouti a cikin makon da ya gabata har ya suma, kuma sun karya masa awaza har guda 4 sanadiyyar haka. Jaridar ‘The National’ ta kasar Amurka bayyana cewa Barghouti yana daga cikin shuwagabannin Falasdinawan da Hamas ta bukaci a sakeshi a musayar fursononi na baya bayan nan. Dansa Arab Barghouti ya ce ya samu labarin irin halin da mahaifinsa yake ciki a hannun HKI daga bakin falasdinawa guda 5 da aka saka sannan aka koresu zuwa kasar Masar. Barghouti dan shekara 66 a duniya ya fara gwagwarmaya da HKI tun yana dan shekara 15 a duniya. A shekara 1987 yahudawa sun koreshi...
	Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa. Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci. Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato October 16, 2025  Manyan Labarai Sauya Sheƙa: Diri Da Wasu Na Guje Wa Matsalolin Da Suka Ƙirƙiro – Dickson October...
	Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban kasar Paul Biya da ya amince da shan kaye. Ministan harkokin cikin gidan na kasar Kamaru ya zargi Issa Bakari da cewa yana da wani shiri na kokarin kona kasar Kamaru ta hanyar taimakon kasashen waje. A makon da ya shude ma dai Atanga Nji ya yi gargadi kar wanda ya fitar da sakamakon zaben, domin yin hakan zai zama daidai da cin amanar kasa....
	Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne.   Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.”   Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa...
	More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba.   Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba. NAJERIYA A YAU: Shin...
 
	Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji  October 15, 2025  Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025  Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025 
	  A yayin shari’ar, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, sai dai kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da shaida wadda ta gamsar da ita ba tare da wata shakka ba. Mai shari’a Dahiru ya ce laifin ya ci karo da sashe na 284 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta yin jima’i ba bisa ka’ida ba, don haka ya yanke wa Hayatu Muhammad hukuncin daurin shekaru hudu a kan kowanne daga cikin tuhumomin biyu, wanda zai fara ne tun ranar da aka kama shi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Labarai Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar October 15, 2025  Labarai Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar...
 
	Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025  Daga Birnin Sin Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar October 15, 2025  Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles October 15, 2025 
 
	Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
	An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka.   Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama.   “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani.     “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
	  Sanarwar ta fito ne daga Daraktan yada labarai na kungiyar, Ahmad Hamisu Gwale yau Laraba 5 ga watan Oktoba, 2025. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14, 2025  Wasanni NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars ₦9.5m, Ta Rage Mata Maki 3 Da Ƙwallaye 3 October 13, 2025  Wasanni Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano October 13, 2025
	Rahotanni sun bayyana cewa rikici na kara Kamari tsakanin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan inda dakarun sojin kasar Pakistan suka sanar da cewa sun tarwatsa tankokin yakin kasar Afghanistan guda 6 kuma an samu mummunar asara a cikin dakarunta a arangama da aka yi a yankin Kurram. Bayan tsagaita wuta na dan wani lokaci fadan ya sake rikicewa  tsakanin dakarun sojin Pakistan da na mayakan Taliban, inda Islam abad ta zargi Kabul da bada mafaka ga kungiyoyin yan ta’adda dake kawo rashin zaman lafiya a yanki, arangamar da akayi a baya bayan nan ta nun irin tashin hankali da ake ciki a iyakokin kasashen biyu Kakakin sojin kasar Pakistan ya bayyana cewa dakarun kungiyar Taliban sun kaddamar da hari kan...
	  A ɓangaren hauhawar farashin abinci a watan Satumba na 2025, ya dawo kashi 20.9 cikin 100 a maimakon kashi 37.77 cikin 100 a cikin watan Satumban 2024 ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025  Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025  Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025
	Ministan harkokin wajen kasar Iran Abass Araqchi ya bayyana yadda wasu kasashen turai 3 suka yi amfani da yarjejeniyar JCPOA da kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya wajen mayar da kudurin kwamitin da aka soke shi a baya kan kasar iran, wanda ya fuskanci adawa daga kasashe da dama ciki har da mambobin biyu na dindindin a kwamitin sulhu a matsayin dokar da ta sabama doka kuma ba za ta yi tasiri a shari’a ba. Kasashen turai saboda matsin lambar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA don haka wadannan kasashe basu da hurumin da za su ce wani abu kan jarjejeniyar,  tun da saboda su ne da Amurka dukkan yarjejeniyar ta wargaje Minista Araqchi ya bayyana cewa batun yankin...
	Kwamandan rundunar ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa nuna kwarewa da juriya, inda ya bukace su da su ci gaba da sharar daji har sai an kakkaɓe duk wasu masu aikata laifuka gaba daya a jihar Taraba.   Ya bayyana ci gaba da jajircewar rundunar sojin Nijeriya wajen tabbatar da tsaro da tsaron duk ‘yan kasa masu bin doka da oda, yana mai ba da tabbacin cewa, sojojin za su ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da al’ummomin yankin domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Labarai Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu October 15, 2025  Manyan...
	  Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da Patrick Herminie wajen aiwatar da sakamakon taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC a matsayin wata dama ta ci gaba da daukaka dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa manyan matakai da kara kyautatawa jama’arsu. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya October 14, 2025  Daga Birnin Sin Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani October 14, 2025  Daga Birnin Sin Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka...
	Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya bayyana Jihar Borno a matsayin jiha mafi juriya a Najeriya, yana jaddada gagarumar nasararta wajen shawo kan ƙalubale da dama tsawon shekaru. Yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Isa Kadafur, a Maiduguri, Ministan ya yaba wa mutanen jihar bisa jajircewarsu da himmarsu wajen fuskantar matsaloli. Wannan ziyara na daga cikin shirye-shiryen taron Kwamitin Kwamishinonin Yada Labarai na jam’iyyar APC. Ya bayyana cewa abubuwan da suka faru a Borno cikin shekaru goma da suka wuce sun nuna jarumtaka da haƙurin mutanen jihar, waɗanda ke ci gaba da ginawa da tafiya gaba duk da matsalolin da suka fuskanta. Ministan ya jaddada cewa ƙarfin gwiwar mutanen Borno abin alfahari...
	Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa. Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025  Labarai Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu October 15, 2025  Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025
	’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata. Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike Shaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa. Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga...
	Kwamatin harkokin lafiya na majalisar dokokin jihar Jigawa ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar da ta kafa asusun adashen gata na kiwon lafiya na jihar ya sahalewa asusun damar samo kudade daga wasu bangarori da ba na gwamnati ba. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya yi wannan tsokaci lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a ofishin asusun da ke Dutse.  Ya bayyana bukatar ganin asusun JICHIMA ya nemo kudade daga hannun masu taimakon al’umma da cibiyoyi da ‘yan siyasa da kwamitocin zakka da na waqafi domin bunkasa asusun, ta yadda zai biya bukatun kiwon lafiyar al’ummar jihar. Alhaji Usman Musari ya lura cewar fadada hanyoyin samun kudade ga...
	Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fadawa kungiyar Hamas su mika makamansu da radin kansu ko kuma zai kwance damararsu da karfi. Jaridar Daily Mails ta kasar Burtaniya ta nakalto shugaban yana fadarwa kafafen yada labarai a washinton a jiya Talata. Amma kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makamai a zirin gaza ta bakin mataimakin babban sakataren kungiyar Mohammad Al-Hindi a hirar da yayi da tashar talabijan ta Aljazeerah cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a gaza basu amince su mika makamansu a yarjeniyar sulhu na Trump ba kuma basu damu da barazanar shugaba Trump na kwance damarasu da karfi ba. Alhindi ya kara da cewa banda haka babu wata kalma ko guda a cikin yarjeniyar da...
	Wani babban jami’in kungiyar Hamas a gaza ya bayyana cewa HKI tana dakile kokarinda kungiyar take na nemo da kuma mayar da gawakin yahudawan Sahyoniya da suka halaka saboda barin wutan da sojojin ta suka  yi kan gaza, wanda ya kai ga mutuwar jami’ansu da suka bawa aikin kula da yahudawan. Don haka wannan ya sa suka rasa samun wadan nan jami’insu saboda sun mutu, sun kuma mutu tare da yahudawan da suke hannunsu. Kungiyar Hamas bata san a dai dai inda suke ba a lokacinda aka kashe su, don haka akwai bukatar lokaci kafin su gano wadannan mutane. Wasunsu sun karkashin burmudhin gine-gine a gaza wanda yake bukatar kwacesu kafin a kai ga gawakinsu. Don haka lai gwamnatin yahudawanne...
	Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kungiyar kwallon kafa ta kasaSuper Eagles murnar nasarar da suka samu ta ci 4 da nema a kan Cheetahs ta Jamhuriyar Benin, tare da yabawa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na ci gaba da kokarin cika al’umma, yayin da suke neman cancantar zuwa gasar cin Kofin Duniya ta FIFA a shekarar 2026. Shugaban ƙasar ya jinjina wa Super Eagles bisa ƙwazo, da jajircewar da suka nuna a filin wasa na Uyo, yana mai cewa wannan gagarumar nasarar ta sake karfafa ‘yan Najeriya kan harkar ƙwallon ƙafa. “Yanayin farin ciki da ake ciki a fadin ƙasar nan na nuni da yakinin da muke da shi  cewa Najeriya ta cancanci samun gurbi a gasar...
	Yansanda a kasar Italia sun kara da masu zanga zanga masu kuma goyon bayan Falasdinawa, don hana a gudanar da wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta HKI da kuma ta kasar Italia a filin wasa na Udine a jiya Talata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Italia ta aika yansanda fiye da 1000 guda, tare da jiragen sama masu saukar ungulu don hana masu zanga –zangar isa filin wasan. Labarin ya kara da cewa zanga-zangar wacce kwamitin masu goyon Falasdinawa ya shirya. Zanga-zangar don hana wasan ta ilimunation wato fidda goni na masuhalattar gasar duniya ta FIF 2026. Daga karshe  dai an yi gasar kuma kasar Italiya ta lallasa HKI da 3-0....
	Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci. Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan cin hanci, domin hana masu rashawa samun wajen ɓuya. “Mu tabbatar babu inda ɓarayi za su ɓuya. Duk wanda yake tayar da hankali a ƙasashenmu bai kamata ya samu natsuwa ba,” in ji Fagbemi. Ƙungiyar NACIWA ƙungiya ce ta hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen ECOWAS, wadda ke aiki tare wajen yaƙi da rashawa. Shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne Ola Olukoyede, wanda kuma...
	“Kusan kullum muna cikin tashin hankali a Shinkafi,” in ji shi. Mutumin ya kuma zargi gwamnati daga matakin tarayya har zuwa ƙaramar hukuma da zuba wa matsalar ido. “Hare-haren suna ci gaba a Birnin Yero, Jangeru, Shanawa, da Shinkafi kanta. Ko jiya da safe sun kawo hari sun kama manoma.” A cewarsa, manoma da dama sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron za a sace su. Wasu kuma suna zuwa da dare ne kawai don samun ɗan abin da za su ci. Sai dai, gwamnatin Jihar Zamfara ta ce tana sane da matsalar da jama’ar yankin ke fuskanta, kuma tana ɗaukar matakai don magance ta. Mai magana da yawun gwamna, Mustafa Jafaru Kaura, ya ce: “Gwamnati tana yin duk abin da...
	‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu. “Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam. “Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Sojoji Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace A Kwara October 15, 2025  Manyan Labarai Dalilin Da Ya Sa Mutane Ke Dawowa Jam’iyyar APC — Shettima October 15, 2025  Labarai Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria  October 14, 2025
	Kasar Iran ta yi Allah wadai da kalaman kin jinin Iran da Trump ya yi a majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da zarge-zarge marasa tushe da kuma da’awar rashin gaskiya da rashin kunya da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan Iran, wanda ya yi a ranar Litinin a zauren majalisar dokokin yahudawan sahayoniya a gaban masu aikata laifukan kisan kare dangi. A cewar wani rahoto da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar a jiya Talata, sanarwar ta ce: Amurka a matsayinta na kasar da ta fi kowacce kasa samar da ayyukan ta’addanci a duniya, kuma mai goyon bayan gwamnatin sahayoniyya ‘yan...
 
	A Lokacin Yaki, Iran Ta Tarwatsa Wata Cibiyar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya Da Ke Yankin Farar Hula
	Iran ta kai hari a wani sansanin sojan Isra’ila na sirri da ke karkashin wata hasumiya a Tel Aviv Yankin Gray, wani dandali ne na bincike, ya bayyana samuwar wani maboyar sirri na sojan Isra’ila da ke karkashin wani hasumiya a Tel Aviv, wanda ake kyautata zaton yana cikin wadanda aka kaiwa hari da makami mai linzami na Iran yayin harin da aka kai ranar 13 ga watan Yuni. Bisa binciken da aka gudanar, dandalin ya gano wurin da wani wurin karkashin kasa da aka fi sani da “Site 81”, wani rukunin jami’an leken asiri na hadin gwiwar sojojin Amurka da Isra’ila da ke karkashin rukunin gidaje na Da Vinci a wata unguwa mai yawan jama’a a tsakiyar birnin Tel...
	Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro  ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi. Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau. Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000....
 
	Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci
	Babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falasdinu ya jaddada cewa: ‘Yantar da sauran fursunonin manufa ce da ba za ta fice daga muhimman abubuwan da suka aka sa a gaba ba Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul- Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya tabbatar da cewa: Ba za a taba mantawa da manufar ‘yantar da sauran jajirtattun fursunonin Falasdinu daga gidajen yarin ‘yan mamayar yahudawan sahayoniyya ba saboda yana daga cikin muhimman abubuwan da ‘yan gwagwarmaya suka sa a gaba. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Today cewa: Kwamandan al-Nakhalah ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar litinin cewa: Tutocin gwagwarmaya suna ci gaba da wanzuwa a kasa...
	“Salon shugabancinsa da amincewa da cancanta sama da son rai ne ya sa kowane mai kishin ci gaba daga ƙarshe yake samun mafaka a APC,” in ji shi. Gwamna Mbah ya bayyana shiga jam’iyyar APC bayan tattaunawa da magoya bayansa, yana mai cewa hakan “sabuwar tafiya ce” ga Jihar Enugu da yankin Kudu maso Gabas wajen samun babban matsayi a siyasar ƙasa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta October 14, 2025  Manyan Labarai Majalisar Wakilai Ta Buƙaci Hukumomin Tsaro Su Kai Agajin Gaggawa A Sakkwato October 14, 2025  Siyasa PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai October...
	More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya.   Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na cigaba da yi mata dabaibayi. Shin ko hakan na nufin jam’iyyar ta fara gushewa ne a siyasar Najeriya? NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
	Sojoji sun kama wata mata da mijinta da suka yi kaurin suna wajen safarar makamai a yankin Saminaka da ke Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna. Dubun ma’auratan ta cika ne a wani shingen binciken inda sojojin Rundunar Operation Fansan Yamma suka gano harsasai 1,207 hannunsu. Kakakin rundunar, Manjo Samson Zhakom ya ce an kama su ne a hanyars ta kai wa ’yan ta’addan da ke addabar yankin Arewa maso Yamma makaman. Ya ce matar mai shekaru 18 mijin masi shekaru 40 suna tsare suna amsa tambayoyi, yana mai jinjina wa sojoji da ’yan banga bisa kwarewar da suka nuna wajen kama miyagun. Kofin Duniya: Da sauran rina a kaba duk da Najeriya ta ci Jamhuriyar Benin 4-0 Na yafe...
	Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026. Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta. Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa. A gaba kuma, an hada Victor Osimhen da Akor Adams domin tayar da kura. Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika...
	Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne, Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin. Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira...
 
	Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata
	  Ta ce shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, duk suna kira ne da a yi hadin gwiwa don tabbatar da daidaiton jinsi, ya zama bai daya cikin manyan batutuwa da ya dace a tattauna a duniya. Ana bukatar karin ayyuka, kuma ba shakka wannan taro yana da matukar muhimmanci.   A nata bangare kuwa, wakiliyar kasar Tanzaniya Juliana Kibonde, cewa ta yi, an saurari jawabin shugaba Xi Jinping, wanda ke da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka. An kuma lura da yadda za a ba mata ikon ci gaba a fannoni kamar na fasaha, da siyasa da sauyin yanayi. Kazalika, shugaba Xi ya ambaci batun gibin dijital, kuma ana iya fahimtar cewa, wasu kasashe suna...
	Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin  sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim. Ga yadda hirar ta kasance: Gabatar da kanki ? Sunana Rukaiya Abdullahi Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood? Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020. Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim? To  da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato...
	’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...
	Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Kampala babban birnin kasar Uganda don halattan taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwammu karo 19 . Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran za’a gudanar da taron ne tare da neman ‘shi’arin “zurfafa hadin kai da kuma rabon fahintar juna a duniya’. Ana saran Jami’an dublomasiyya da jakadu daga kasashe duniya 120 ne zasu halarci taron karo na 19 a birnin Kampala. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baghaei ya bayyana cewa banda tattaunawar wadan nan kasashe a tsakaninsu kan al-amura da dama, a gefen taron kuma kwamitin Falasdinu na kungiyar zai gudanar da taronsa, wanda gwamnatin JMI take cikinsa. A taron dai ana saran ministan...
	Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa jami’an tsaron JMI suna cikin cikken shiri na kare kasar daga makiya, a duk lokacinda ta sake farma kasar da yaki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baghaei yana fadar haka a jiya litinin a taron yan jaridu da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Ya kuma kara da cewa JMI zata saurari shawarorin kawayenta amma kuma tana cikin shirin ko ta kwana idan makiya sun yi kuskure sun fadawa kasar da yaki. Baghaei ya na nuni ne da zantawar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a makon da ya gabata, inda kuma ya bukaci shugaba...
	“Idan mutum ya shiga jarrabawa kuma Allah Ya kawo dama ta afuwa, dole ne ya yi farin ciki. Ni da iyalina da masoyana mun yi murna ƙwarai,” in ji Lawan. “Na gode wa Allah da kuma Shugaba Tinubu saboda ya yi abin da ya kamata a yaba masa.” Ya bayyana cewa rayuwa a gidan yari ta koya masa juriya da fahimtar cewa komai ƙaddara ce. “Tun kafin na bar kotu na sallama komai ga Allah. Na sani cewa duk inda mutum ya samu kansa, akwai darasi a ciki,” in ji shi. Bayan fitowarsa daga gidan yari, Faruk Lawan ya sauya tafiyarsa ta siyasa. Ya ce ya rabu da tafiyar Kwankwasiyya da aka san shi da ita, duk da cewa har...
 
	Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara
	Sakataren Majalisar Koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana haka ne a  wani sako da ya walalfa a shafinsa na sadarwa dangane da sako fursunonin Falasdinawa da aka yi. Haka nan kuma ya ce: ‘Yan Sahayoniya sun ga hotunan gagarumin tarbar da aka yi wa Fursunonin Falasdinawan da hakan yake sake tabbatar da cewa; Kungiyar Hamas da gwagwarmaya suna da karbuwa da farin jini a tsakanin Falasdinwa bayan gushewar shekaru biyu na kazamin yaki. A jiya da safe ne dai al’ummar Falasdinu su ka tarbi Falasdinawan da aka HKI ta sako daga gidajen kurkukunta a karkashin yarjejeniyar kawo karshen yaki da ta kunshi musayar fursunoni. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up...
	More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shekara da shekaru kungiyar malaman jami’oi ASUU ta kwashe ta na gudanar da yajin aiki ba tare da samun biyan bukata ba.   Irin wannan yajin aiki da kungiyar malaman ke shiga ya jefa dalibai da malaman da ma harkar ilimi cikin halin ni ‘yasu a Najeriya. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa DAGA LARABA: Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wasu hanyoyin da kungiyar malaman ASUU za ta iya bi don warware matsalar ta ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba. Domin sauke shirin, latsa nan
	Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) ta mayar da martani kan barazanar gwamnatin tarayya ta “ba aiki, ba a biya”, tana mai cewa ba za ta bari a tsoratar da ita da irin wannan gargaɗi ba. Shugaban ASUU, Chris Piwuna, ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a shirin Politics Today a ranar Litinin. Piwuna ya ce ASUU ta tsaya tsayin daka tare da sauran ƙungiyoyin Malamai kamar CONUA, da NAMDA, da SSANU, da NASU, wajen goyon bayan yajin aikin da ke gudana. Ya zargi Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, da ƙoƙarin rarraba malamai ta hanyar yin alƙawarin biyan wasu ma’aikata albashi. “Ya na ƙoƙarin rarraba kan mu, amma kan mu a haɗe yake. Babu wanda...
	A yau litinin ne kungiyar Al-qassam brigades bangaren soji na kungiyar Hamas ta mika yahudawa guda 7 daga cikin guda 20 da ta kama su take rike da su ga hukumar kula da bada a gaji ta duniya a yankin Gaza Kungiyar hamas ta cika alkawarin da ta dauka na mika sauran mutane da take tsare da su  domin nuna gaskiyar aniyarta na kulla yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro a yankin Gaza, duk da yake cewa Isra’ila ta kafa  tarihin cin amana da rashin cika alkawari kan duk wata yarjejeniya da aka kulla tsakaninta da alummar falasdinu. Wannan shi ne zangon farko na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma bayan shiga tsakani da aka yi a sharma El-shaikh...
	Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esma’il Baqahea yayi gargadin game da barazanar da ake fuskanta na bazuwar fadan da ake yi a kan iyaka tsakanin  kasar Afganistan da kuma kasar Pakistan, a yankin, inda dukkan bangarorin biyu suke musayar wuta a wurare daban daban dake kusa da iyakokin kasashen. Yace babban abin da ke da muhimmanci a wajen mu shi ne batun tsaro da zaman lafiya a kasashen dake makwabtaka da su, kasashen Pakistan da Afghanistan  yan uwan mu ne musulmi dake makwabtaka da mu, kuma ya yi amanna cewa duk wani kace-nace tsakanin kasashen biyu to zai iya fantsama zuwa wasu kasashe, Jamhuriyar musulunci ta Iran  ta yi kira ga kasashen biyu da su koma teburin tattaunawa, kuma...
	Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu. Ana ta bangaren Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar...
	Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
	Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu.  “A cikin sa’o’i 24 da...
	Shugaban kasar Amurka Donal Trunp ya isa HKI a safiyar yau Litinin, inda ake  saran zai yi jawabi a majalisar dokokin HKI, kafin ya wuce zasu Sharm sheikh na kasar Masar inda zai halarci bikin sanyawa yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da kuma HKI wanda aka fara aiki da shi a wannan makon. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto hotunan bidiyo kai tsaye daga Telaviv a lokacinda jirgin shugaban kasar ya sauka, sannan shuwagaban HKI  da kuma firai ministan HK Benyamin Natanyahu ne suka tarbe shi a tashar jiragen sama na Bengerion. Shugaban ya iso HKI a dai dai lokacinda kungiyar Hamas ta mika fursinonin HKI 7 ga kungiyar Red Cross a zirin Gaza. Wanda daya...
	Labaran da suke fitowa daga kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross ta fara karban fursinoni yahudawa daga hannun kungiyar Hamas kamar yadda aka tsara. Tashar talabijan ta Almayadeen ta bayyana cewa kungun fursinoni yahudawa masu rai 7 ne kungiyar ta Karba daga dakarun Hamas a yankin da ake kira Nitsarin a tsakiyar zirin gaza, da misalign karfe 8 na safe a yayinda gungu na biyu kuma wanda ya kunshi yahudawa 10 masu rai kungiyar Agajin ta karbesu a garin Khan Yunus dake areacin gaza da misalign karfe 10 na safe. Labarin ya kara da cewa an ga motocin bas -bas suna isa kurkukun da ake tsare da falasdinawa. Sannan ana saran yahudawan zasu...
	Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
	An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya. Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse. Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben. Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka...
	  Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.   Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su...
	Na farko, hada kai don samar da yanayi mai kyau ga ci gaban mata. Na biyu, a karfafa abubuwan da za su habaka ingancin ayyukan mata cikin hadin kai. Kana na uku, a gina tsarin kare hakkin mata tare. Sai na hudu, a bude sabon babin hadin gwiwa tsakanin mata a duniya.   Za a gudanar da taron kolin mata na duniya a yau da gobe Talata a birnin Beijing. Kuma tuni shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, suka yi musafaha da shugabannin tawagogin kasashe, da kungiyoyin duniya da suka halarci taron, tare da daukar hotuna tare da su. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A...
	A safiyar Litinin ɗin nan ƙungiyar Hamas ta saki rukunin farko na ’yan ƙasar Isra’ila bakwai da ta yi garkuwa da su a Zirin Gaza. A ɗaya ɓangaren kuma Falsɗinawa sun yi cincirindo a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan domin tarbar ’yan uwansu kimanin 2,000 da Isra’ila za ta sako. Tuni jami’an kungiyar agaji ta Red Cross suka shiga gidan yarin Wada a safiyar domin ɗaukar wani fursuna Bafalasdine da za fitar, wanda ke fama da rashin lafiya. Hamas ta mika su ne ga kungiyar Red Cross a Gaza a yayin da ake da ran sako wasu ƙarin mutum 13 na gaba a Litinin ɗin nanm a cewar hukumomin Isra’ila. Wannan na faruwa ne a yayin da Shugaban Amurka, Donald...
	Shugaban kasar Amurka ya yi barazana ga shugaban kasar Rasha na aike wa Ukraine makamai masu linzami kirar Tomahawk Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: Zai gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin cewa: Akwai yiwuwar Ukraine za ta iya samun makamai masu linzami kirar “Tomahawk” idan Rasha ba ta kawo karshen yakin Ukraine ba. Da aka tambaye shi a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da Masar da yammacin ranar Lahadi ko shi da kansa zai tattauna da Putin kan batun, Trump ya ce, “Yana iya magana da shi. Yana cewa: Idan ba a warware wannan yakin ba, zai aika wa Ukraine da makamai masu linzami na Tomahawk.” Trump ya kara da...
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025  Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025  Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025 
	  ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025  Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025  Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025
	Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
	ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan October 12, 2025  Daga Birnin Sin Sharhi: Lai Qingde Ba Zai Iya Jirkita Gaskiya Ba October 12, 2025  Daga Birnin Sin Wang Yi: Sin Na Maraba Da Dukkanin Matakai Na Dawo Da Zaman Lafiya A Gaza October 11, 2025 
	Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.   Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA  Daga Birnin Sin Sharhi:...
	Yau Lahadi  al’ummar Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar. Masu kada kuri’a miliyan takwas ne aka tantance domin kada kuri’a a zaben zagaye na farko da Shugaban kasar mai ci Paul Biya mai shekara 92 dake neman wa’adi na takwas. A cikin makonni biyu na yakin neman zaben, Shugaba Biya wanda aka dade ba a gan shi a bayyanar jama’a ba ya gudanar da gangami guda daya kacal, a garin Maroua dake yankin Arewa mai Nisa, daya daga cikin yankuna uku na arewa, inda ya sha alwashin magance matsalar tsaro da rashin aikin yi. A hukumance dai ‘yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a wannan zaben, amma biyu sun janye. Manyan masu kalubalantar Paul Biya guda...
	Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere.   Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha.   Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru.   Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
	Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar. Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi. Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata. “Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana. RN    
	A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?   A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
 UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba