Aminiya:
2025-11-14@21:58:45 GMT

’Yan Majalisar Tarayyar Kaduna 3 sun sauya sheka zuwa APC

Published: 14th, October 2025 GMT

’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.

Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi.

Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP.

Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka.

Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila

Jim kadan bayan sanar da sauya shekar tasu ce Gwamna Uba Sani ya jagorance su zuwa ga shugaban majalisar inda suka dauki hoto kafin shi da tawagarsa su wuce.

Tuni dai Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Kingsley Chinda, ya kalubalanci sauya shekar, yana mai kira ga shugaban majalisar da ya kwace kujerunsu, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: sauya sheka sauya shekar

এছাড়াও পড়ুন:

HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kaduna, ta ƙone fiye da tan 52,000 na miyagun ƙwayoyi a bainar jama’a a ƙauyen Karofi da ke Kufena, a kan tsohuwar hanyar Birnin Gwari da ke Zariya.

An gudanar da bikin ƙone kayan ne a wannan Alhamis ɗin, inda Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd.), Shugaban NDLEA kuma Babban Jami’in Gudanarwa, ya jaddada cewa hukumar ta duƙufa domin kawar da barazanar miyagun ƙwayoyi daga cikin al’umma.

Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu

Ya bayyana cewa, “Miyagun ƙwayoyi suna lalata tarbiyyar matasa a hankali, ba tare da an farga ba. Kowace tan ɗaya da aka ƙone, an ceto rayukan mutane da dama daga halaka.”

Shugaban hukumar, wanda Mataimakin Daraktan Harkokin Miyagun ƙwayoyi, Suleiman Ningi, ya wakilta, ya yi gargadi ga masu safarar miyagun ƙwayoyi da su daina kasuwancin kayan haram, su koma safarar kayan halal, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Janar Marwa ya ce NDLEA na ci gaba da fatattakar manyan dillalan miyagun ƙwayoyi da ƙungiyoyin su, tare da ƙarfafa wayar da kai a kan illolin kayan laifi.

Ya yaba wa rundunar NDLEA ta Jihar Kaduna bisa ƙoƙarinta, tare da gode wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, saboda goyon bayan da yake bayarwa, ciki har da ba da motocin aiki da fili domin gina bariki ga hukumar.

Shugaban NDLEA ya roƙi iyaye, shugabannin al’umma da na addini, da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan mutane kan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa, “Yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi yaƙin ceto rayuka da makomar ƙasa ne.”

Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna, Mohammed Tukur, ya bayyana cewa bikin ƙone miyagun ƙwayoyi na nuna jajircewar hukumar wajen kare al’umma daga illolin sha da safarar su.

Ya ce wannan mataki shi ne “ƙarshe a jerin matakan aiwatar da doka”, domin tabbatar da cewa waɗannan ƙwayoyi masu haɗari sun ɓace gaba ɗaya daga hannun mutane, don hana su cutar da matasa ko ƙarfafa ayyukan laifi.

Kwamandan ya bayyana cewa miyagun ƙwayoyin da aka ƙone sun haɗa da Tramadol, Wiwi (Cannabis), da Hodar Iblis da an kiyasta darajar su za ta kai Naira biliyan biyar.

Ya bayyana cewa wannan gagarumar nasara ta samu ne sakamakon ƙoƙarin jami’an NDLEA tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro irin su sojoji, hukumar kwastam, DSS, da ‘yan sanda.

Ya ce, “Wannan aiki shaida ce ta gaskiya, riƙon amana, da ƙwarewar NDLEA. A yau, muna sake tabbatar da sakonmu cewa Jihar Kaduna ba mafakar masu safarar ko masu amfani da miyagun ƙwayoyi ba ce.”

Tukur ya jaddada biyayyarsu wajen dawo da zaman lafiya da kare makomar matasan jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Uba Sani ya yaba wa NDLEA bisa ƙoƙarinta wajen ganin cewa an tsarkake Jihar Kaduna daga miyagun ƙwayoyi.

Gwamnan ya ce yawan ƙwayoyin da aka ƙone na nuna tsananin ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da doka a jihar, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin tsaro wajen yaƙi da laifuka da duk wata barazanar tsaron al’umma a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP
  • Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030
  • HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya
  • Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
  • Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
  • Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo rancen N1.15bn
  • Majalisar Jihar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Kan Laifin Rashin Ɗa’a
  • Majalisar Kogi Ta Dakatar Da Shugaban Ƙaramar Hukuma Bisa Zargin Rashin Ɗa’a
  • Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
  • Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Sagir Ƙoƙi ya fice daga NNPP