Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar.

Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu.  “A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ni da mataimakin shugaban kwamitin tattaunawa na gwamnatin tarayya, mun tattauna da ASUU, zan iya gaya muku a yau, a zahiri, an biya kusan dukkan bukatun ASUU, don haka ban ga dalilin da ya sa ASUU ta fara yajin aikin ba.” In ji Ministan ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano October 13, 2025 Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025 Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa  yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan  Nuwamba a jihar.

Shugaban  Hukumar Kula  Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya,  tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.

Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.

Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.

Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.

A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.

Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.

Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.

Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.

Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.

Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.

Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • Iran ta yi tir da matakin Australiya na alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila