’Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun sace dabbobi a Katsina
Published: 15th, October 2025 GMT
’Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da sace dabbobi da dama a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin, inda aka kashe wani mazaunin ƙauyen Kwadawa da ke yankin Gachi, yayin da wani kuma ya jikkata.
Gwamnan Bayelsa ya fice daga jam’iyyar PDP Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincikeShaidu sun ce kimanin ’yan bindiga 100 ne suka kai harin, inda suka kuma mamaye ƙauyen Bogga; ƙauyen Fulani da ke kan hanyar Kankia zuwa Ingawa.
Sakamakon haka, mazauna ƙauyukan Bogga, Taiba Badole, Arahiya Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo duk da ke yankunan Gachi da Fakuwa/Kafindangi, sun tsere daga gidajensu saboda tsoron hare-hare.
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun koma Kankia bayan da aka samu yarjejeniyar zaman lafiya a wasu ƙananan hukumomi maƙwabta, lamarin da ya sa suka faɗaɗa hare-harensu zuwa yankunan Charanchi da Kusada.
Wani mazaunin yankin mai suna Haladu Badole ya ce: “Kwana uku da suka gabata mun fara lura da motsin wasu mutane da ba mu saba gani ba, sannan a daren jiya suka kai hari suka kwashe dabbobinmu.”
Mutanen yankin sun roƙi hukumomi da su tura jami’an tsaro domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.
Yankin gabashin Kankia, ya kasance cikin zaman lafiya, sai dai kwanan nan an fara samun hare-hare a yankunan Rimaye, Magam, Sukuntuni, Gyaza da Kunduru.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Sadik Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Amma ya ce rundunar ta fara bincike kuma tana ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hari
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba.
Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa ta diflomasiyya, Araqchi ya ce shi ko shugaba Pezeshkian ba za su iya tunkarar wadanda suka kai wa al’ummar Iran hari da kuma ci gaba da yi mata barazana da kuma sanya mata takunkumi.”
Ya kara da cewa: Duk da haka, Iran tana maraba da duk wani shiri da zai kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza da kuma bukatar kai wa ga janye sojojin mamaya daga yankin.
Araqchi ya jaddada cewa: Falasdinawa suna da ‘yancin fahimtar ainihin hakkinsu na cin gashin kansu, kuma dukkan kasashe, fiye da kowane lokaci, suna da alhakin taimaka musu tare da goyon bayan wannan bukata ta doka da ta dace.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci