Yadda Najeriya ta casa Jamhuriyar Benin 4-0
Published: 14th, October 2025 GMT
Tawagar Super Eagles ta Najeriya sun kara da Cheetahs na Jamhuriyar Benin a wasan neman cancantar shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da suka fafata a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Jihar da Uyo ya kasance tamkar mai zafin gaske kuma an nuna bajinta.
Tun kafin a fara wasan, an samu sauye-sauye hudu daga tawagar da ta doke Lesotho, inda Wilfred Ndidi ya hau matsayin kyaftin, yayin da Moses Simon ke shirin yin buga na 85 a wasannin kasa da kasa.
Wasan ya fara da sauri — ina minti na uku kacal, Osimhen ya zura kwallo ta farko bayan Chukwueze yi mika masa. Cheetahs sun yi kokarin farkeaw a minti na 12, amma Calvin Bassey ya dakile harin.
Na yafe wa Maryam Sanda —Mahaifin Bilyaminu Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya AbdullahiA minti na 22, Osimhen ya kusa kara ci, amma dan wasan baya na Benin ya hana shi. Sai dai a minti na 38, Chukwueze ya sake aika masa da wata kwallo, kuma Osimhen bai yi wata-wata ba — ya zura ta biyu! Najeriya 2, Benin 0.
Bayan hutun rabin lokaci, Benin sun fara da matsa lamba, amma Osimhen ya sake daukar hankalin duniya — inda a minti na 51, ya cika hat-trick dinsa! Kwallo ta uku ke nan a hannunsa.
Super Eagles sun ci gaba da matsa lamba, inda suka nemi ci na hudu a minti na 68, amma Ndidi ya kasa cin kwallon da aka buga masa.
A minti na 90 Onyeka ya zura wa Super Eagles kwallon Najeriya na hudu a ragar Jamhuriyar Benin.
Wannan wasan ya nuna cewa Osimhen ba dan wasa bane kawai — jarumi ne, gwarzo ne, kuma jagora ne a fagen kwallon kafa.
Najeriya na kan gaba a wannan fafatawa, kuma alamu na nuna cewa Super Eagles na kan hanya madaidaiciya zuwa Kofin Duniya ta 2026.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi
Rukaiya Abdullahi mawakiya ce a Masana’antar Kannywood wacce daga bisani kuma ta dawo yin fim duk a masana’antar. A hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara aiki a matsayin sakatariya ta ofishin daya daga cikin masu shirya fim.
Ga yadda hirar ta kasance:
Gabatar da kanki ?
Sunana Rukaiya Abdullahi
Yaushe kika shigo Masana’antar Kannywood?
Na shigo Masana’antar Kannywood a shekarar 2020, amma zan samu kamar shekara 15 ina tare da su sai dai ban fara yin fim ba sai a 2020.
Me ya jawo hankalinki kika shigo harkar fim?
To da farko dai ba harkar fim na fara da ita ba a Kannywood, na fara da aikin sakatariya ne a wurin ’yan fim, yayan Nasiru Sarkin waka wato Musbahu Ahmad to shi ne wanda ya dauke ni aiki a matsayin sakatariya. To sakamakon akwai babana Ibrahim Mandawari shi ne bayan na nuna masa sha’awata ta yin fim to sai ya tambaye ni shin fim nake son yi ko aiki da ’yan fim? To sai na ce masa ina sha’awar yin fim ne. Sai ya ce to tunda ina sha’awar yin fim akwai wanda zai hada ni da shi ya ba ni aiki tukuna. Sai na ce ba komai ko ma aikin ya ba ni zan yi, sai ya fada min to akwai abokinsa sakataren MOPPAN Alhaji Salisu Ofisa zai yi magana da shi.
Sai ya kira shi, ya yi masa Magana, ya fada masa cewa zai turo masa wata ’yarsa. Haka ya tura ni, na je na samu Alhaji Salisu Ofisa a matsayin ’yarsa a Industry din, daga nan ne kuma sai na zama sakatariyarsa.
Wato dai da aikin sakatariya kika fara a Kannywood kafin ki koma ki rika fitowa a fim. Haka ne?
Eh haka ne, daga nan ban koma na fara fim ba sai bayan shekara 2, to a can dai sai ni ma na fara koyon waka, kuma ina ma’amala da ‘yan fim masu zuwa ofishinsa, wasu in sun zo haka muna hira da su sai su rika tambaya ta ke ’yar fim ce ?
To wata rana akwai wani darakta Ahmad Jifa da ya ce wa Alhaji Salisu sakatariyarka ta ce za ta yi fim, shi kuma sai ya ce eh, ta ce min tana sha’awar shiga fim. To ba zan manta ba, wata rana ina zaune sai Musbahu ya kirawo Ofisa ya ce ya turo masa sakatariyarsa ga wani gurbi da za ta hau a fim, shi ne da na je sai Musbahu ya ce min ke kin ce kina sha’awar yin fim, to ga wata dama da za a ba ki, ki fara fitowa a fim din, sai na ce to ina murna na tafi.
Da kika ce kin fi yin waka a fim, wakar ita ta fi rinjaya ko fim?
Gaskiya na so yin harkar fim, to sai dai na dawo ina tunanin ko Allah ne bai yi akwai abincina a harkar fim ba, ban sani ba sai wakar dai ta rinjayi fim din. Ni kuma ga shi zuciyata tana ga fim din, ina son a kira ni a ba ni aiki.
Yi bayanin irin wakokkin da kika yi yadda duk wanda ya karanta wannan labari zai iya gane cewa lallai ke ce?
Yawwa wakar da na fara farkon ita ce wakar Kwankwaso, a lokacin yana APC, sai na yi ta Buhari (marigayi tsohon Shugaban kasa ) to daga ta Buhari sai ta Sarkin Biu sannan na yi wa Dan Majalisar Jiha kuma na yi wa Dan Majalisar Taraiya shi ma dai na Biu din.
Duk da kina Kannywood a iya cewa waka ta rinjayi yin fim?
Gaskiya wakokin da na yi sun fi finafinan da na yi yawa.
Kin ce kina fitowa a matsayin ’yar tijara a fim, ko za ki yi mana bayanin ma’anar tijara a fim. Me hakan yake nufi ?
Tijara tana nufin ina fitowa a matsayin masifaffiya, wato a mafi yawan finafinai a wannan matsayin aka san ni. Ita wannan tijara ina yin ta ne da mazajena wato mijina a fim.
Yi mana karin haske dangane da irin tijarar da kike yi a fim?
Ina fada da mazajena, wato duk wanda ya gani ana so ya fahimci halayemu daban-daban, wata mafadaciya ce wata kuma mai hakuri ce kuma ni a karan kaina ba haka nake ba, kuma mazajen da nake yin fada da su, ina fada da su ne a saboda ba sa yi min adalci. Kuma irin rashin adalcin da suke yi min shi ke bata min rai har nake yi musu tijara. Wato ba ni da hakurin da zan jure abin da suke yi min.
Wannan darasi na yin tijara da kike yi a fim, ko yana yin tasiri ga mata masu irin wannan hali wadanda ake yi abin domin su suka kalla, kuma ya mazan naki ke kasancewa a fim din?
Gaskiya su ma mazajen biye min suke yi su fada, in fada
Kuma auren yana yin karko?
Aure yana karko halayya ce ta irin wasu matan ake nunawa da yadda za a yi hakurin zama da su da halinsu shi ne cin ribar zamantakewar.
A wadannan shekaru da kika yi a Kannywood wadanne irin kalubale kika fuskanta ta bangaren iyaye ko ’yan uwan ko al’umma?
Eh, to gaskiya ni dai ban samu wani kalubale daga gida ko yan uwana ba ko wasu mutane daban da ba iyayena ba. Iyayena tunda na taso ina kyautata musu kuma mu 9 ne a dakinmu, maza guda 3 nake bi, amma a cikinsu ba zan ce na fi su ba amma ni ce mafi kyautata wa iyayenmu kuma iyayenmu suna da kyakkyawan zato a kaina. Da na ce musu zan yi fim sai suka ce to Allah Ya ba ki sa’a
A al’adance idan aka kira ki da suna Delu za ki amsa sunan ko?
Insha Allahu ko Kande ko Delu idan aka kira ni sunana ne zan amsa.
Nasarori fa?
Eh to gaskiya na samu nasarori Alhamdulillahi. Babbar naasarar da na samu saboda tun da da na zo Industry din nan gaskiya ban samu wani abu ba na akasi ba har zuwa yanzu, kullum ci gaba nake samu
Wane kira za ki yi wa ‘yan Kannywood da kuma masu kallon fim din ki?
To ni babban kiran da zan yi musu shi ne ya kamata ‘yan Kannywood a rika tausayin juna, akwai dattawan gaske da ya kamata a ce ana taimakawa da wasu daga cikinmu ‘yan Kannywood ta fuskar taimakon juna musamman kamar mu na kasa-kasa kamata ya yi a ce suna sama su taimake mu. Amma sai ka ga kullum mai akwai shi suke taimaka mawa mara shi kuma ba a taimaka masa. Wato sai dai a kara wa mai karfi karfi.