Shugaban Kasar Columbia Ya Yi Dirar Mikiya Kan Donald Trump Kan Bai Wa Isra’ila Makamai
Published: 15th, October 2025 GMT
Shugaban Kasar Columbia Ya Soki Donald Trump Akan Bai Wa Isra’ila Makamai
Shugaban na kasar Columbia Gustavo Petro ya ce, Bugun kirjin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi na bai wa “Isra’ila” makamai tare da cewa ta yi amfani da su da kyau, ba wani abu ne da ya cancanci a yi masa tafi, sunan shi tarayya a aikata laifi.
Shugaba Gustavo Petro yana mayar da martani ne akan zancen da shugaban kasar Amurka ya yi a Majalisar “Knesset’ ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya ce; Isra’ilan ta yi amfani da makaman da ya ba ta da kyau.
Shugaba Gustavo ya kara da cewa; wadannan makaman na Amurka sun kashe mutane 70,000 sannan kuma sun jikkata wasu 200,000.
Shi dai shugaban kasar ta Columbia yana daga cikin na gaba-gaba wajen sukar lamirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila saboda yakin Gaza da kuma Amurka wacce take goya mata baya.
A lokacin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na karshen nan, shugaba Gustavo Petro ya shiga cikin masu Zanga-zanga a birnin Newyork domin nuna goyon bayan Gaza da kuma yin kira da a kawo karshen yaki. Haka nan kuma kasarsa ta yanke huldar diplomasiyya da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
A wani jawabinsa na bayan fagen taron na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira da a kafa rundunar kasa da kasa domin ‘yanto da Falasdinu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Ce; ‘Yantar Da Fursunonin Falasdinawa Abu Ne Mai Muhaimmanci October 15, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70 October 15, 2025 Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba October 14, 2025 UNDP : An ruguza fiye da kashi 80 cikin 100 na gine-ginen Gaza October 14, 2025 Sojojin Madagaska sun karbe mulkin kasar October 14, 2025 Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu October 14, 2025 Islamic Jihad : jarumtakar ‘yan gwagwarmaya ce ta haifar da sako fursunonin falasdinawa October 14, 2025 Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAM October 14, 2025 Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata October 14, 2025 Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Madagaska sun karbe mulkin kasar
Rahotanni daga Madagaska na cewa sojoji sun sanar da karbe mulki bayan arcewar shugaban kasar Andry Rajoelina.
Kanar Michael Randrianirina ya sanar a gaban fadar shugaban kasar cewa sojoji sun kwace mulki, da rusa majalisar dattawa da kuma babbar kotun tsarin mulkin kasar, yayin da ya bayyana yadda za a kula da majalisar dokokin kasar.
Hakan dai na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar tsige shugaba Andry Rajoelina da gagarumin rinjaye.
Sojojin na CAPSAT sun kuma sanar da cewa, suna kafa majalisar shugabannin kasa, wanda ya kunshi jami’an soji da na Jandarmomi kadai.
A ranar 25 ga Satumba, ne aka fara zanga-zangar a Madagascar, kan katsewar ruwa da wutar lantarki wanda ya rikide zuwa bore wa gwamnati.
Shugaban kasar Andry Rajoelina, mai shekaru 51, ya yi kokarin shawo kan masu zanga zangar saidai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, har zuwa lokacin da aka ga wasu sojoji sun shiga suna marawa masu zanga zangar baya.
Bayanai sun ce a ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin sojin Faransa ya fitar da shugaban kasar Andry Rajoelina daga kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu October 14, 2025 Islamic Jihad : jarumtakar ‘yan gwagwarmaya ce ta haifar da sako fursunonin falasdinawa October 14, 2025 Aragchi Yana Uganda Don Halattan Taron Ministocin Kungiyar NAM October 14, 2025 Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata October 14, 2025 Ma’aikatar Harkokin wajen Kasar Iran Ta Yi Tir Da Jawabin Trump A Knesset Ta HKI October 14, 2025 An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia October 14, 2025 Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025 October 14, 2025 Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci